Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Shugaban Kare Hakkin Dan Adam Na Majalisar Dinkin Duniya Yace RSF Sun Aikata Zalunci
Published: February 13, 2026 at 8:29 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

A yau ne ofishin babban kwamishinan sashen kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk ya ce rundunar ‘yan tawayen Sudan ta RSF sun aikata zalunci matuka da ya karya dokokin yaki lokacin da suka kwato birnin al-Fashir, da kuma yiwuwar aikata laifi na cin zarafin bil-adama.

Birnin na al-Fashir da ke yankin Dafur ya fada hannun ‘yan tawayen ne a watan Octobar bara bayan da dakarun su suka dade suna kewaye da wajen, abin da ya jawo kisan dubbannan mutane.

A hira da aka yi da fiye da mutane 140 da abun ya shafa a arewacin Sudan da kuma gabashin Chad, Ofishin rajin kare hakki na Majalisar Dinkin Duniya ya bada bayanin cewa fiye da mutane 6000 sun rasa rayukan su a kwanaki ukun farko da dakarun RSF suka far ma al-Fashir.

Volker Turk ya kara jaddada kiran sa ga wadanda ke da ruwa da tsaki su dauki matakan da ya kamata don kawo karshen take dokoki da dakarun dake karkashin su suke yi. Ya kuma bukaci kasashe da ke da tasiri su dauki matakin gaggawa don dakile sake afkuwar irin abin da ya faru a al-Fashir.

Afrika, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Hukumar Zaben Najeriya Ta Sanar Da Ranar Zaben Shugaban Kasa
Next Post: Hukumar Hakar Ma’adanai A Kasar Zambiya Ta Dakatar Da Ayyukanta

Karin Labarai Masu Alaka

Kasashen Turai: Bazamu Yarda Da Dokar Harajin Trump Ba Labarai
Kasar Malawi Ta Kaddamar Da Rigakafin Shan Inna Kiwon Lafiya
Afirka Ta Kudu Ta Kubutar Da ‘Yan Kasar Da Suke Taya Sojojin Rasha Yaki Afrika
Najeriya: Ba Don Leken Asiri Muka Tura Jirgin Yakin Mu Ba Afrika
Shugaba Trump Ya Amince Da Tsawaita Cinikayya Tsakanin Amurka Da Kasashen Afirka Afrika
Yakin Gabas Ta Tsakiya Ya Kawo Cikas Ga Cinikin Nama A Kenya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Fiye Da Mutane 200 Sun Rasa Rayukansu A Wajen Hakar Ma’adanai Labarai
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojoji Sun Murkushe ‘Yan Bindiga A Jihar Sakkwato Labarai
  • Onana Ba Ya Cikin Tawagar Kamaru (AFCON) Wasanni
  • Pakistan Da Afghanistan Sun Shiga Kwana Na Biyar Suna Fafatawa Afrika
  • Kamfanin Magani Na Aspen Yayi Gagarumar Asara A Cinikayya Afrika
  • Kenya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kasar Rasha Afrika
  • An Ga Watan Ramadan A Najeriya Da Nijar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.