Shugaba Donald Trump na Amurka ya kara wasu kasashe 7 cikin kasashen da gwamnatinsa zata haramta ma ‘yan kasar shiga kasar Amurka, cikinsu har da ‘yan Jamhuriyar Nijar.

Fadar White House ta fada ranar talata cewa, shugaba Trump ya sanya hannu a kan wata takardar sanarwa ta karawa da karfafa jerin kasashen da za a sanya ma al’ummarsu takunkumin shiga Amurka a saboda tabbatar da cewa ba su bincika ko bayar da bayanai ga hukumomin Amurka ta yadda zasu iya kare tsaron kasa daga irin wadannan mutane da zasu shigo kasa daga wadannan wurare.
Wannan matakin na ranar talata, a bayan haramta ma ‘yan Jamhuriyar Nijar shigowa Amurka, zai kuma kara da ‘yan kasashen Burkina Faso, Mali, Sudan ta Kudu, Sham ko Syria, da kuma wadanda suke rike da takardun tafiye-tafiye na hukumar mulkin Falasdinu.
Har ila yau wannan matakin yanzu ya haramta shigowar dukkan ‘yan kasashen Saliyo da Laos, wadanda a baya an takaita shigowarsu ne kawai.
Wannan sabon haramcin zai fara aiki daga ranar 1 ga wata mai zuwa na Janairu.
Sanya kasar Sham cikin jerin kasashen na zuwa ne duk da alkawarin da Trump yayi na cewa zai yi duk bakin kokarinsa na ganin kasar ta samu nasarar shawo kan matsalolinta a bayan tattaunawar da yayi da shugaban kasar, Ahmed al-Sharaa, wanda a can baya kwamanda ne na kungiyar al Qaida wanda Amurka ta taba sa takunkumi a kansa.
Fadar White House ta gabatar da hujjar cewa mutanen kasar Sham da suke shigowa Amurka suna ci gaba da zama har bayan karewar takardun bizar su, tana mai cewa dalilinta na daukar wannan matakin a kan Sham ke nan.


