Tsagera ‘yan Bindiga a Mali masu alaka da al-Qeada sun kashe direbobin manyan motocin dakon mai 10 da yaran gidan su biyu, yayinda suke balaguro a yankin Kayes da yake yammacin Mali a karshen watan daya, kamar yadda Kungiyar kare hakkin Bil’adama Human Rights Watch ta fada a ranar talata.
Kungiyar da ake kira Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin ta kai hari kan jerin gwanon motocin dakon mai 40 da sojoji suke baiwa kariya, kamar yadda Kungiyar ta Human Rights ta fada.
Kungiyar ‘yan bindigar mai lakabiin JNIM a takaicce galibi tana aika-aikanta ne a Mali da Burkina Faso, yanzu ta zama babbar Kungiyar ‘yan Bindiga a yankin. Wai tana da burin kafa tsarin shari’a a fadin yankin kasashe da suke yankin Sahel, kuma ta fadada ikonta zuwa yammacin Afirka. Hukumomin Mali yanzu suna raka Motocin dakon mai domin saukaka karancin mai da fitinar ‘yan bindigar ta janyo a kasar da bata da kogi.


