Wasu ‘yan bindiga sun kashe sojojin Najeriya guda tara tare da jikkata wasu da dama a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin ƙasar, kamar yadda majiyoyin tsaro da jami’an gwamnati na yankin suka bayyana a ranar Laraba.
Jihar Kebbi, wadda ke da iyaka da ƙasashen Benin da Nijar, na daga cikin jihohin arewa maso yamma inda kungiyoyin ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane ke yawo cikin sauƙi, tare da yin mu’amala da ‘yan ta’addan Islama da ke ƙara faɗaɗa tasirinsu a yankin.
Majiyoyin soja guda biyu da wani mazaunin yankin sun ce sojojin na sintiri ne a kusa da sansaninsu a ƙaramar hukumar Shanga ta jihar Kebbi, lokacin da ‘yan bindigar suka kai musu hari da daddare a ranar Talata.
Majiyoyin sojan sun ce suna zargin kungiyar ‘yan ta’adda ta Lakurawa, wadda aka san tana aiki a yankin tare da kai hare-hare kan jami’an tsaron Najeriya.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya tabbatar da faruwar harin bayan ya ziyarci sojojin da suka jikkata, amma bai bayyana adadin wadanda suka mutu ba.
Matsalar tsaro ita ce babbar ƙalubalen da ke gaban gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, kusan shekaru uku bayan hawansa mulki.
Rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa nan take ba dangane da lamarin.


