Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • An Horar Da Mata Kan Sarrafa Abinci Mai Gina Jiki A Gombe Afrika
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika

’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
Published: September 10, 2026 at 6:23 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe ta ce ta samu gagarumar nasara a ayyukan da take gudanarwa na yaƙi da garkuwa da mutane, ’yan bindiga, safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka a faɗin jihar.

Rundunar ta ce a ranar 8 ga Satumba, 2026, da misalin ƙarfe takwas na safe, jami’an ’yan sanda, sojoji, Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), ’yan banga da mafarauta, ƙarƙashin jagorancin Jami’in ’Yan Sandan Sashen Dukku, sun gudanar da samame a wasu maboyar miyagu da ake zargi a yankin Kowagel na Ƙaramar Hukumar Dukku da kuma wasu sassan Bojude a Ƙaramar Hukumar Kwami.

A yayin samamen, jami’an tsaron sun kama wani mutum mai suna Manu Alhaji Sani, mai shekaru 30, ɗan ƙauyen Wawa a Ƙaramar Hukumar Funakaye, wanda rundunar ta bayyana a matsayin wanda ake zargi da kasancewa cikin ƙungiyar masu garkuwa da mutane.

Rundunar ta ce yayin binciken farko, wanda ake zargin ya amsa cewa yana da hannu a wasu ayyukan garkuwa da mutane da aka gudanar a ƙananan hukumomin Dukku, Kwami da Funakaye, tare da wasu ’yan ƙungiyarsa da har yanzu suke kan gudu.

Bayan kama shi, jami’an tsaron sun ƙara matsa lamba tare da ci gaba da gudanar da bincike da samame a yankin. A cewar rundunar, wannan matakin ya tilasta wa sauran ’yan ƙungiyar tserewa, inda suka bar mutane uku da suka yi garkuwa da su.

Daga bisani jami’an tsaron sun kuɓutar da mutanen ukun, waɗanda suka haɗa da Hauwa Alhaji Sani, mace mai shekaru 44; Aishatu Alhaji Sani, yarinya mai shekaru 16; da Umaru Alhaji Sani, yaro ɗan shekaru biyu.

Rundunar ta ce dukkansu mazauna ƙauyen Jonde, da ke Ƙaramar Hukumar Dukku ne.

A yayin samamen, jami’an tsaron sun kuma kwato babur ɗin Honda mai lambar rajista BBB 29 UT, da kuma wayoyin hannu masu maballan guda uku.

Rundunar ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin cafke sauran waɗanda ake zargi da suka tsere domin tarwatsa ƙungiyar masu aikata laifukan gaba ɗaya.

An Kama Wanda Ake Zargi da Safarar Tramadol

A wani ci gaba kuma, a ranar 8 ga Satumba da misalin ƙarfe tara na safe, jami’an Safer Highway Patrol, tare da haɗin gwiwar Operation Hattara, sun kama wani mutum da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Rundunar ta ce jami’an, waɗanda ke aikin sintiri a kan hanyar Liji zuwa Biu, sun samu sahihin bayanan sirri, inda suka tare wata motar Peugeot 406 mai launin shuɗi, mai lambar rajista YDB 48 FL.

Bayan binciken motar, jami’an sun kama wani mutum mai suna Mohammed Abdullahi, wanda aka fi sani da ‘Babangida’, mai shekaru 37, ɗan Bomala Quarters a Gombe.

Rundunar ta ce binciken motar ya kai ga gano sachets 2,500 na ƙwayoyin Tramadol masu nauyin milligram 100 kowacce.

Mohammed Abdullahi da kayan da aka kwato suna hannun ’yan sanda, yayin da bincike ke ci gaba domin gano inda ƙwayoyin suke zuwa da kuma sauran mutanen da ka iya kasancewa cikin harkar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya yaba wa jami’an tsaro bisa haɗin gwiwar da suka nuna wajen gudanar da ayyukan, tare da jinjinawa jajircewarsu, ƙarfin hali da kuma gaggauta ɗaukar mataki bisa sahihan bayanan sirri.

Kwamishinan ya sake jaddada aniyar rundunar na ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro da suka dogara da bayanan sirri domin yaƙi da garkuwa da mutane, ’yan bindiga, safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka a jihar.

Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su kasance cikin ƙarin taka-tsantsan, tare da gaggauta sanar da jami’an tsaro duk wani abin da suke zargi ko kuma bayanin da zai taimaka wajen dakile ayyukan masu aikata laifuka.

Rundunar ta bayar da lambobin wayar gaggawa 0815 056 7771 da 0903 643 5359 domin jama’a su kai rahoton duk wani abin da suka lura da shi.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
Next Post: Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu

Karin Labarai Masu Alaka

Majalisar Wakilai Tayi Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Gombe Labarai
Bayan Shekaru Biyar, Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Gano Motar da Aka Sace A Fatakwal Afrika
Samar Da Albarkatun Mai Ya Ragu A Iraq Afrika
Jami’an Tsaron Pakistan Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Labarai
Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Dawo Da Kudaden Ma’aikata Afrika
An Kamallah Jigilar Alhazain Najeriya Domin Hajjin 2026 Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Tinubu Ya Nemi ‘Yan Najeriya Su Sake Zaɓensa A 2027
  • An Horar Da Mata Kan Sarrafa Abinci Mai Gina Jiki A Gombe
  • Hukumomin Tarayya A Gombe Sun Yi Alƙawarin Tallafa Wa Ci Gaban Tattalin Arziki
  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Iran Ta Tasa Keyar Wani Jirgi Shake Da Mai Sauran Duniya
  • Ukraine Takai Hari Wajen Kera Makami Mai Linzami A Rasha Labarai
  • Ƙungiyar Mata Sunyi Kira Ga Jam’iyar P R P Da Ta Dauki Baheejja A Matsayin Mataimakiyar Gwamnan A Bauchi 2027 Labarai
  • Gwamnatin Jihar Neja Ta Soke Lasisin Mallakar Wasu Manyan Filaye A Jihar Labarai
  • Kotu Ta Bada Belin Kwamishinan Kudin Jihar Bauchi Najeriya
  • Kasar Israela Zata Gina Sansani A Gaza Afrika
  • Babu Alamar Tsagaita Wuta A Yakin Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Koriya Ta Arewa Ta Gudanar Da Gwajin Makami Mai Linzami Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.