Bam ya Fashe a wani masallaci a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a Nigeria, yayin da ake tsaka da gabatar da sallar Magariba, har yanzu de ba’a san adadin mutanen da suka jikkata ko suka rasa rayukan su ba.
Fashewar bom din ya auku a jihar da tayi shekaru tana fama da hare-haren ‘yan ta’adda irin su Boko Haram, da kungiyar ISWAP, da yayi sanadiyar dubbannan rayuka, kuma da yawa suka tsere daga gidajen su, a arewa maso gabashin Najeriya.
Ba wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin, amma ‘yan ta’adda sukan kai hare-haren Kunar bakin wake, ko su saka bom a masallatai da wurin dandazon jama’a a Maiduguri.

Tun a shekarar 2009 ne kungiyar Boko Haram ta fara tada hankali a Borno, inda take so ta kafa daular Musulunci amma duk da mai da martani da sojoji ke yi, da kuma hadin kan yankuna wajen kawo karshen ta, kungiyar na ci gaba da kai hare-hare da ke barazana ga rayukan mutane a arewa maso gabas.


