‘Yan tawayen kungiyar M23 masu samun goyon bayan Rwanda sun ce zasu janye daga garin Uvira na yankin gabashin Kwango ta Kinshasa, a bisa rokon da gwamnatin Amurka ta yi musu.
Gwamnatin shugaba Trump ta bayyana kama wannan gari da ‘yan tawayen suka yi a makon da ya shige a zaman matakin barazana ga kokarin yin sulhu a yankin.
‘Yan tawayen sun kwace garin na Uvira dake bakin iyakar Kwango da Burundi, kasa da mako guda a bayan da shugabannin kasashen Rwanda da Kwango suka gana da shugaba Trump a birnin Washington domin rantaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya.
A ranar asabar sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, yace take-taken Rwanda a yankin gabashin Kwango sun keta haddin yarjejeniyar zaman lafiyar Washinton, ya kuma lashi takobin daukar matakan tabbatar da cewa sassan sun cika alkawuran da suka dauka.
Rwanda ta musanta cewa tana tallafawa ‘yan tawayen na M23, tana mai zargin sojojin Kwango da na Burundi da laifin sake barkewar fadan.
Rahoton da wasu kwararru na MDD suka rubuta a watan Yuli, yace kasar Rwanda ce take ba da umurni tare da tsara dukkan ayyukan ‘yan tawayen.


