YANBINDIGA SUN KASHE MUTUN GUDA TARE DA YIN GARKUWA DA MUTANE KIMANIN 100 A JIHAR NEJAN NAJERIYA.
Yanzu haka dai Yanfashin d
aji na ci gaba da tafka ta,asarsu a Wasu sassanan jihohin Najeriya Lamarin dake kara jefa alumma cikin Yanayi na zaman dar dar.
Rahotanni Daga Jihar Neja na nuna cewa Yanfashin Dajin sun yi awon gaba da Mutane kimanin 100 tare da Kashe guda a Yankin gulbin Bola ta karamar Hukumar Mariga,
Wani Mazaunin Yankin da ya Bukaci a sakaya sunanshi Yace yanzu Kwanaki Uku kenan Basu kwana a gidajensu..
To kokarin Jin ta bakin rundunar Yansanda ta jihar Neja akan wannan Sabon hari yaci tura Domin kokarin Samun kakakin yandan Wasu Abiodun ta wayar Salula yaci tura.
Amma Shugaban karamar Hukumar ta Mariga Hon.Aliyu Bagga ya Tabbatar da Aukuwar Lamarin harma yayi jaje ga Al’ummar Yankin na Mariga.
Ta’azzarar Ayyukan yanbindigar a Jihar Nejan dai yasa ko a wannan rana ta Asabar Dubban Al,ummar Musulmi suka hallara a babban Masallacin idi na Garin Kontagora Domin gudanar da Addu,ar neman sauki daga Allah…

