Ranar litinin tsohon fira ministan kasar Malaysia, Najib Razak, zai san ko zai iya karasa sauran hukuncin daurin da aka yanke masa a gidansa, ko kuma a cikin kurkuku.
An yanke ma Razak hukuncin daurin shekaru 12 a gidan kurkuku a shekarar 2022, bisa laifin zarmiya da cin hanci a badakalar da aka fi sani da sunan abin Fallasa na 1MDB.
A shekarar da ta shige, wata hukumar yahudawa dake karkashin jagorancin tsohon Sarkin Malaysia, ta rage masa hukumcin zuwa shekaru 6.
Amma Razak ya ce Sarkin na Malaysia ya kuma bada umurnin cewa yana iya karasa wannan hukuncin a gidansa, watau daurin talala, kuma abinda ya sa ya shigar da kara ke nan a kotu yana neman a yi aiki da wannan umurnin da gwamnatin fira minista Anwar Ibrahim ta ce ba ta san da shi ba.
Jami’an gwamnati sunyi wata da watanni suna cewa ba su da wata masaniya game da wannan takardar umurni, duk da cewa a cikin wannan shekara, ofishin tsohon sarkin da ma wani lauya na tarayya sun gaskata cewa lallai an bayar da takardar umurnin rege hukumcin zuwa shekaru 6, kuma za a iya kyale ya karasa a gidansa.
Ranar litinin, babbar kotun birnin Kuala Lumpur zata yanke hukumci a kan wannan, kwanaki hudu kafin ta yanke hukunci a kan shari’a mafi girma da shi Najib yake fuskanta dangane da wannan abin fallasa na asusun 1Malaysia Development Berhad, wanda asusu ne na kudin gwamnati da ya taimaka wajen kirkirowa a shekarar 2009.
Masu fashin baki suka ce mutane ba zasu yi murna ba, musamman magoya bayan fira minista Anwar, idan kotun ta wanke shi a wancan zargin, Anwar dai ya ci zabe ne bisa alkawarin yaki da cin hanci da rashawa.


