Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ Afrika
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u Afrika
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa Afrika
  • Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa Afrika

Dangantaka Tayi Tsamari Tsakanin Salah Da Slot.
Published: December 8, 2025 at 7:30 PM | By: Bala Hassan

Dangantaka Tayi Tsamari Tsakanin Salah Da Slot,

Dangantakar ta kara Tsamari ne bayan da Kocin Liverpool, Arne Slot ya cire jeren sunayen tawagar da za ta fafata da Inter Milan, ba tare da Salah ba, bayan dan wasan dan Ƙasar Masar yayi wasu kalamai masu tayar da hankali a kwanaki da suka haifar da rikici a Anfield.

An cire fitaccen dan wasan Liverpool Mohamed Salah daga tawagar da za ta fafata da Inter Milan a gasar zakarun Turai wadda hakan ya tada sabon rikici da kocin Arne Slot.

Tsohon dan wasan a Anfield, wanda ya taka rawar gani wajan samun nasarar Liverpool a gasar Premier a kakar wasa ta bara a karkashin Slot, yanzu yana fuskantar makoma mara tabbas a kulob din hakan na kara ruruwa wutan rikici a bayan fage.

Majiyoyin da ke kusa da ƙungiyar sun bayyana cewa rikicin da ya ɓarke ​​tsakanin Salah da Slot ya wargaza dangantakar da ta daɗe tana tsakanin ɗan wasa da koci bayan wani rahoto daga Fabrizio Romano cewa za a iya cire ɗan wasan na Masar.

Hakan ta biyo bayan maganar da Salah ya yi bayan da aka ajiye shi a benci  karo na uku a jere ciki harda wasan da Liverpool tayi da Leeds United, inda kalaman bai yi wa Slot daɗi ba, wanda hakan ya haifar da rashin jituwa da masu sharhi suka bayyana a matsayin “wanda ba zai iya gyaruwa ba.”

Wannan rashin jituwa ya yi tsanani har aka cire Salah daga tawagar Liverpool da za ta je Italiya don fafatawa da Inter Milan UCL, wanda hakan ke nuna sako a bayyane daga shugabannin ƙungiyar.

Duk da Salah ya atisaye da ‘yan uwansa, magoya bayan Liverpool suna mamakin wannan mataki, ganin yadda Salah ya kasance ɗaya daga cikin manyan ‘yan wasan ƙungiyar da kuma muhimmiyar rawar da ya taka a kakar wasansu ta Zakarun Turai.

Rashin ɗan wasan gaban na Masar ya haifar da manyan tambayoyi game da alkiblar ƙungiyar da kuma yadda suke shirin durkusar da hazakarsa a gaba.

Yayin da wannan labarin ke ci gaba da bayyana, magoya bayan Liverpool suna jira don sanin ko tauraron dan wasansu zai iya murmurewa daga wannan rikicin.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Nuhu Ribadu Ya Mika Dalibai 100 da Aka Ceto Ga Gwamnatin Jihar Neja
Next Post: Shugaba Tinubu: Naji Dadin Sako Daliban Neja Da Aka Sace

Karin Labarai Masu Alaka

Wikki Tourists FC: Ta Yi Sabbin ‘Yan Wasa Uku Wasanni
Najeriya Na ƙoƙarin Shiga Gasar Cin Kofin Duniya 2026 Ta Barauniyar Hanya Wasanni
Sarkin Gombe Yayin Hawan Tudun Wada Labarai
FIFA, Ta Raba Jaddawalin Rukuni Na Gasar Kofin Duniya 2026. Wasanni
Wasu Zakaru Da Suka Samu Karramawar Hukumar CAF Ta Afrika Wasanni
An Kaddamar Da Kwamitin Kwallon Kafa A Tsakanin Masarautun Jihar Gombe Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa
  • Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa
  • Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Yohanna YD Buru: Makon Haɗin Kan Addinai Ya Ƙarfafa Ilimin Zaman Lafiya A Najeriya Labarai
  • Usman Maiyama Ne Gwarzon Kamun Kifin Argungu Bana Labarai
  • Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Zata Tabbatar Da Tsagaita Wuta A Kwango Afrika
  • ‘Yan Ta’adda Sun Tarwatsa Wani Kauye A Jihar Sakkwato Tsaro
  • Tattalin Arzikin Kasar Bahrain Ya Bunkasa Sakamakon Ruruwar Masu Yawon Bude Ido Labarai
  • Kasar Ghana Zata Sauya Inda Take Kai Sarrafa Gwal Afrika
  • Anyi Janazar ‘Yan Shi’a 33 Da Aka Kashe A Masallacin Juma’a Sauran Duniya
  • Hukumar NDLEA Ta Lalata Gonakin Wiwi A Ekiti Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.