Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa Afrika
  • Tinubu Ya Buɗe Katafaren Kamfanin Sarrafa Lithium Domin Bunƙasa Tattalin Arziki Afrika
  • Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ Afrika
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u Afrika
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa Afrika

Sojojin Kasar Isra’ila Sun Kashe Wani Babban Kwamandan Hamas
Published: December 14, 2025 at 6:17 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar sojojin bani Isra’ila ta ce ta kashe wani babban kwamandan Hamas mai suna Raed Saed, a harin da ta kai kan wata mota ranar asabar a birnin Gaza.

Wannan shine kisa na wani babban dan kungiyar Hamas na farko tun lokacin da aka kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Oktoba.

A wata sanarwar hadin guiwa, firaminista Benjamin Netanyahu da ministan tsaron kasar sunce an kai hari a kan Saed ne a bayan wani harin da Hamas ta kai da nakiya ta raunata wasu sojojin Isra’ila biyu ranar asabar.

Hukumomin kiwon lafiya a Gaza sun ce harin da Isra’ila ta kai kan motar a birnin gaza ya kashe mutane biyar, ya raunata wasu akalla 25. Amma ba a ji daga bakin kungiyar Hamas ko ma’aikatan kiwon lafiya a kan ko akwai Saed a cikin wadanda aka kashe ba ya zuwa yanzu.

A cikin wata sanarwar da ta bayar, hamas tayi Allah wadarai da wannan harin a zaman wanda ya keta yarjejeniyar tsagaita wuta, amma ba ta tabbatar da ko akwai Saed a cikin wadanda aka kashe ba, haka kuma ba ta yi barazanar daukar fansa ba.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Tattalin Arzikin Kasar Bahrain Ya Bunkasa Sakamakon Ruruwar Masu Yawon Bude Ido
Next Post: Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Borno

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Gombe Ta Kaddamar Da Sabon Ofishin GOGIS Don Inganta Tsarin Filaye Afrika
Masana Lafiya – Preeclampsia Cuta Ce Mai Hadari Amma Ana Iya Magance Ta Afrika
Isra’ila Tace Bazata Sake Kai Hari Kan Cibiyar Gas Ta Iran Ba Afrika
Kasar Afirka Ta Kudu Ta Gayyaci Sabon Jakadan Amurka Afrika
Baba Malam Ya Lallasa Abokan Hamayya Da Kuri’u Sama Da Dubu 236 A Zaben Fidda Gwani Afrika
Iran Ta Rufe Sararin Samaniyar Ta Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa
  • Tinubu Ya Buɗe Katafaren Kamfanin Sarrafa Lithium Domin Bunƙasa Tattalin Arziki
  • Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Fubara Yana Yiwa Dimokraɗiyya Zagon Kasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Congo Ta Kawo Karshen Cutar Kyandar Birai Afrika
  • Shugaban Kasar Ghana Ya Soki Manufofin Gwamnatin Amurka Afrika
  • Umar Ya Lashe Kyautar Gwarzon ‘Dan-Wasa Na 2025 Wasanni
  • Gwamnan Jihar Gombe Ya Umurci A Rufe Makarantu Labarai
  • Ministan Yaɗa Labarai: Ceto Daliban Neja An Samu Natsuwa A Kasa Labarai
  • CAF Ta Hukunta Samuel Eto’o AFCON 2025 Labarai
  • Sakon Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu A Ranar Dimokraɗiyya Ta 2026 Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.