Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Lumbala Shekaru 30 Bisa Laifin Cin Zarafi
Published: December 17, 2025 at 8:40 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wata kotu a kasar Faransa ta yanke hukuncin daurin shekaru 30 a gidan kurkuku a kan tsohon madugun ‘yan tawayen Kwango ta Kinshasa, Roger Lumbala, wanda ta samu da laifuffukan cin zarafin bil Adama a lokacin yakin Kwango na biyu.

‘Yan rajin ganin an hukumta masu aikata irin wadannan laifuffuka a gadin duniya sun yaba da wannan hukunci a zaman babban ci gaba na hukumta masu hannu a wannan yakin da ya kashe miliyoyin mutane.

A lokacin da yake bayyana hukuncin, alkalin wannan kotu dake birnin Paris, Marc Sommerer, yace Lumbala ya aikata ko ya bada umurnin aikatawa, ko ya tallafa wajen aikata munanan laifuffuka da kashe-kashe da fyade, da gana azaba, da bautarwa da sata da wawusa ko lalata dukiyoyi.

Wadannan laifuffukan da aka tuhumi Lumbala da aikatawa suna da alaka da wani farmakin da wata kungiyarsa mai samun goyon bayan kasar uganda a lokacin, ta kai a shekarun 2002 da kuma 2003 a arewa maso gabashin Kwango.

Sun kai hare-haren ne a kan ‘yan kabilun Nande da Bambuti wadanda suka zarga da laifin goyon bayan wata kungiyar daban ta sojojin sa kai a yankin.

An gudanar da yakin Kwango na biyu daga shekarar 1998 zuwa 2003. Kasashe har guda 9 suka tsoma baki da hannu a wannan yaki, kuma an kashe mutane fiye da miliyan 5, cikinsu har da wadanda suka mutu a sanadin yunwa da kuma cututtuka.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Wani Bayahude Ya Harbe Bafalatsine Dan Shekaru 16
Next Post: Gwamnatin Jihar Yobe: Ana Cin Zarafin Fursunoni A Gidan Gyaran Halin Potiskum

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Gombe Ta Kaddamar Da Sabon Ofishin GOGIS Don Inganta Tsarin Filaye Afrika
Majalisar Dokokin Kamaru Ta Amince Da Wasu Sauye Sauye Afrika
Shugabar Kungiyar Cinikayya Ta Duniya Ta Bukaci Kasashe Su Gyara Harkokin Cinikayya Afrika
Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
Ukraine Zata Sayi Iskar Gas Daga Mozambique Afrika
Tattaunawar Nukiliya Tsakanin Iran Da Amurka Yana Tasirin Akan Farashin Albarkatun Mai Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • EU Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Amurka Da Iran Afrika
  • Jami’ai Daga Amurka Sunce Yakin Amurka Da Iran Zaizo Karshe Amurka
  • Shugaban Ƙasar Djibouti Ya Sake Lashe Zaben Shugaban Kasar Afrika
  • Za’a Fuskanci Bala’in Yunwa A Najeriya Labarai
  • Rundunar Operation Hadinkai Sunyi Nasara Akan ISWAP Da Boko Haram Najeriya
  • ‘Yan Sanda Sunce Mutum Daya Ne Yakai Hare-Haren Jami’ar Brown Da Kuma Na MIT Boston Amurka
  • Shugaban Miyetti Allah Zai Fuskanci Shari’a Kan Zargin Badakalar Kuɗi da Ta’addanci Afrika
  • Iran Zata Kai Hari Tashar Makamashin Ruwa A Gulf Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.