Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Kasar Afirka Ta Kudu Ta Tsare Wasu Amurkawa
Published: December 18, 2025 at 7:27 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Amurka ta yi tur da tsare wasu jami’an ta da kasar Afirka ta Kudu ta yi, wadanda aka ce su na aikin ba da tallafi ga turawan Afirka ta kudu jinsin Afrikaner.

Wani jami’in hukumar kula da shige da ficen baki ta Amurka ya fadawa kamfanin dillancin labaran reuters cewa an tsare wasu jami’an hukumar su biyu na wani dan lokaci, amma an kyale su a ranar talata.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ATK ta ce babu wani jami’in Amurka da aka kama a kasar.

Ranar laraba, hukumomin ATK sun ce sun kama, kuma zasu kori wasu ‘yan kasar Kenya su 7 da suke aiki ba tare da izni ba na taimakawa gwamnatin Amurka wajen tattara takardun neman yin kaura zuwa Amurka na turawan ATK.

Gwamnatin shugaba Donald Trump tana shirin bayar da mafaka ga dubban turawan ATK  Amurka bisa hujjar cewa ana musgunawa ko cin zarafinsu don kawai su turawa ne a kasar, zargin da gwamnatin ATL ta ce babu ko kamshin gaskiya a cikinsa.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Burkina Faso Ta Sako ‘Yan Najeriya 11
Next Post: Kimanin Ganga Miliyan 40 Na Danyen Albarkatun Mai Yayi Kwantai A Kasashen Afirka Ta Yamma

Karin Labarai Masu Alaka

Za’a Saka Tarihin Trump A Manhajar Makarantu Don Jajircewasa Da Kwazo Amurka
Iran: Za A Gudanar Da Jana’izar Khamenei Bayan Kwanaki Goma Na Muharram Afrika
Amurka Tana Cigaba Da Kare Jami’in Da Ya Kashe Ba Amurke Amurka
Na Yi Murabus Ne Don Amurka Ta Keta Haddin Iraniyawa Amurka
Iran Ta Karyata Tattaunawa Da Washington Afrika
Shirin Kwace Iyakar Greenland Da Shugaba Trump Yakeyi Yabawa Kasashen Turai Mamaki Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Masana Lafiya – Preeclampsia Cuta Ce Mai Hadari Amma Ana Iya Magance Ta Afrika
  • Domin Karfafa Tsaro Babban Hafsan Sojin Najeriya Ya Ziyarci Jos Afrika
  • Iran Ta Kama Wani Jirgin Ruwa Shake Da Mai Labarai
  • Shugaban Kasar Madagascar Ya Kori Prime Minista Da ‘Yan Majalisa Afrika
  • An Damke Matasa Masu Gurza Kudaden Ketare Na Jabu Afrika
  • Tinubu: Sojojin Mu Sun Yi Rawar Gani Don Kare Demokuraɗiyya A Jamhuriyar Binin Labarai
  • Iran Da Amurka Zasu Kulla Yarjejeniyar Nukiliya Amurka
  • Ƙungiyoyin Premier 17 Za Su Rasa ‘Yan Wasa 40 saboda Gasar AFCON 2025, Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.