Wakilin Amurka na musamman, Steve Witkoff, yace ana samun ci gaba a tattaunawar da Amurka take yi da Ukraine da kasashen Turai a gefe guda, da kuma wadda take yi da kasar Rasha a daya gefen, duk da nufin kawo karshen yakin Rasha da Ukraine.
Amurka da Ukraine da kuma kasashen Turai sun shafe kwanaki ukun da suka shige suna tattaunawa a jihar florida a kan yadda zasu fito da matsaya guda game da rikicin na Ukraine.
A bayan da suka gana da Kirill Dmitriev, wakilin shugaba Vladimir Putin na Rasha na musamman ran asabar a Miami, Witkoff da mashawarcin Trump, Jared Kushner, sun gana ranar lahadi da wakilan Ukraine da Turai, sannan daga bisani suka gana su kadai da wakilan Ukraine karkashin jagorancin Rustem Umerov.
Witkoff ya fada cikin wata sanarwar da ya rubuta a shafin sada zumunta cewa tattaunawar ta lahadi ta yi ma’ana da amfani, ta kuma mayar da hankali a kan yadda Amurka da Turai da kuma Ukraine zasu tinkari lamarin da murya guda.
A wata sanarwar dabam da ya buga a shafin sada zumunta na X, Witkoff yace Rasha ta nuna cewa har yanzu kudurinta shine na cimma zaman lafiya a Ukraine.
Tunda fari a lahadin, jami’in tsara manufofin hulda da kasashen waje na fadar Kremlin, Yuri Ushakov, yace irin shawarwarin da Ukraine da kasashen Turai suka bayar game da shirin da ake tattaunawa a kai, ba su karfafa guiwar yiwuwar cimma zaman lafiya ba, amma yace an shirya Dmitriev zai koma birnin Moscow yau litinin domin yi masa bayani game da tattaunawar da aka yi.
UShakov yace bayan nan zasu zauna su tsara yadda su ma zasu tunkari lamarin


