Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Jami’an Tsaro: Babu Abun Tashin Hankali Kan Shawagin Jiragen Amurka
Published: December 23, 2025 at 2:29 AM | By: Yusuf Aliyu Harande | Updated: December 23, 2025

Wasu jami’an tsaron Najeriya sun bada tabbaci ga ‘yan kasar cewa babu wani abun tashin hankali ko fargaba gameda jiragen leken asiri na Amurka da suke shawagi a sararrin samaniyar kasar. Suka ce matakin ya faranta musu rai saboda Amurka tana taimakawa Najeriya ne ta fuskar tsaro.

Jami’an tsaron sun tabbatarwa Amurka Ke Magana cewa matakin na hadin gwiwa ne tsaknin jami’an tsaron Amurka da mayakan sama na Najeriya. Suka ce akwai sojojin sama na Najeriya a cikin jiragen da suke aikin leken asirin a sararin samaniyar kasar.

Jiragen suna tashi ne daga Ghana. Wannan matakin ya biyo bayan shawarwari da jami’an gwamnatin Najeriya suka yi da gwamnatin Amurka, bayan da shugaban Amurka Donald Trump, yayi barazanar kai hari kan Najeriya domin kare kiristocin kasar wadanda ake zargin ana yi musu kisn kare dangi. Gwamnatin Trump ta amince zata taimaki Najeriya ne bayan da aka gabatar mata da irin kalubale da kasar take fuskanta ta fuskar tsaro.

Gameda zargin gwamnatin Najeriya tana biyan kudin fansa kamin a saki mutane da ake garkuwa da su, musamman dalibai daga makarantu da ‘yan bindiga suke sace su, jami’an tsaron sun rantse da Allah cewa babu sisin kwabo daga aljihun Najeriya da yake fita domin biyan kudin fansa.

Daga nan suka yi kira ga ‘yan Najeriya su daina yi wa matakan gwamnati bahaguwar fahimta, maimakon haka a kullum su bukaci bayani, kamin su yanke shawara kan batu da  ya shafi gwamnati da al’uma.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya buga labarin zirga-zirgar jiragen leken asirin  sararin samaniyar Najeriya.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: An Samu Nasarar Karbo Karin Yara 130 Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda
Next Post: Afirka Ta Kudu Ta Bayyana Yadda Aka Yaudari ‘Yan Kasar Ake Tilasta Musu Ayyukan Bauta

Karin Labarai Masu Alaka

Tantance Gaskiyar Bayanai Shi Ne Ginshiƙin Aikin Jarida Mai Nagarta – Abdulaziz Afrika
INEC Mayar Da Lokacin Zaɓen 2027 Kafin Azumi Najeriya
Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
Hatsarin Mota Yayi Ajalin Mutum 7 A Gombe Najeriya
Rundunar Sojin Najeriya Ta Dakile Harin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno Labarai
Amurka Ta Yi Juyin Mulki A Kasar Venezuela Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Kama Tsohon Jakadan Birtaniya A Amurka Peter Mandelson Amurka
  • Jagoran Kwankwasiya A Najeriya Ya Koma Jam’iyar ADC Labarai
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino Wasanni
  • Lauya Bala: Tabbas Kotu Zata Soke Zaben Shugaban PDP, Turaki Najeriya
  • Kungiyar MDD Ta Bukaci Ayi Bincike Game Da Kashe ‘Yan Iran Sauran Duniya
  • Pantami Ya Bayyana Dalilin Mayar Da Zaben Sa Abuja Afrika
  • Wikki Tourists FC: Ta Yi Sabbin ‘Yan Wasa Uku Wasanni
  • Gwamna Kefas Na Jihar Taraba Ya Karbi Shaidar Jam’iyar APC Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.