Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Tinubu Yace Zayyi Hadaka Da Kasashen Duniya Domin Kawo Karshen Rashin Tsaro.
Published: January 1, 2026 at 10:44 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ƙara zurfafa haɗin gwiwa da ƙasashen yankin da na duniya a shekarar 2026, domin kawar da dukkan barazanar tsaro da ke barazana ga rayuka, dukiyoyi da kuma cikakken ikon ƙasar Najeriya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabin saƙon sabuwar shekarar 2026 da ya gabatar ga ’yan Najeriya a ranar Alhamis.

Tinubu ya ce tafarkin gyara ƙasar ba abu ne mai sauƙi ba, amma wajibi ne, yana mai jaddada cewa ci gaban tattalin arziki ba zai yi armashi ba tare da tsaro da zaman lafiya ba.

Ya ce Najeriya na ci gaba da fuskantar barazanar ’yan ta’adda da masu aikata laifuka da ke ƙoƙarin dagula zaman lafiyar ƙasa, amma gwamnati na ɗaukar matakan da suka dace domin dakile su.

Shugaban ya bayyana wasu hare-hare da aka kai kwanan nan tare da haɗin gwiwar abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, ciki har da Amurka, domin raunana ƙungiyoyin ta’addanci.

A cewarsa, “A cikin haɗin gwiwa da abokan hulɗa na duniya, ciki har da Amurka, an ɗauki matakai masu ƙarfi kan wuraren ’yan ta’adda a wasu sassan Arewa maso Yamma a ranar 24 ga Disamba.”

Ya ƙara da cewa rundunonin tsaro na ci gaba da kai farmaki kan sansanonin ’yan ta’adda da ’yan fashi a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

Tinubu ya bayyana cewa a shekarar 2026, hukumomin tsaro da na leƙen asiri za su ƙara ƙarfafa musayar bayanai da daidaita ayyuka da abokan hulɗa na yankin da na duniya, domin kawar da duk wata barazana ga tsaron ƙasa.

Ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin tarayya na kare rayuka, dukiyoyi da cikakken ikon ƙasar Najeriya.

Game da gyaran tsarin tsaro, shugaban ya nuna goyon bayan sa ga tsarin ’yan sanda na jihohi, tare da tanadin kariya da tsarin kula da masu tsaron dazuka cikin tsari da ɗa’a ga doka.

A ɓangaren tattalin arziki, Tinubu ya ce sabuwar shekarar za ta kawo wani sabon babi na bunƙasar tattalin arziki mai faɗi, wanda zai shafi rayuwar talakawa kai tsaye.

Ya sanar da cewa za a hanzarta aiwatar da shirin Renewed Hope Ward Development Programme, da nufin shigar da a ƙalla ’yan Najeriya miliyan 10 cikin ayyukan samar da arziki.

A cewarsa, shirin zai bai wa a ƙalla mutane 1,000 a kowace daga cikin unguwanni 8,809 na ƙasar damar samun aikin yi da dogaro da kai, ta fannoni kamar noma, kasuwanci, sarrafa abinci da ma’adinai.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa dukkan manyan ayyukan more rayuwa da ake yi a halin yanzu za su ci gaba ba tare da tsaiko ba.

Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya su fahimci cewa gina ƙasa alhakin kowa ne, tare da ba da gudummawar sa domin cimma manufofin 2026.

A ƙarshe, ya yi addu’ar samun zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a ƙasar, yana mai fatan Allah ya kare ƙasa, ya kiyaye sojoji, tare da hallaka duk masu ƙoƙarin tayar da zaune tsaye.

Shugaban ya yi wa ’yan Najeriya fatan samun sabuwar shekara mai albarka, zaman lafiya da cigaba.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Guinea An Zabi Madugun Sojojin Da Suka yi Juyin Mulki Mamady A Shugaban Ƙasar,
Next Post: Mali Da Burkina Faso Za Su Haramta Wa Amurkawa Izinin Shiga Ƙasashen Su

Karin Labarai Masu Alaka

Dalibai Sun Koma Makarantu A Wasu Jihohin Najeriya Najeriya
Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno Amurka
‘Yan Sanda A Jihar Gombe Sun Karyata Kona Gidan Nafiu Bala Afrika
Hawan Sallah A Jihar Katsina Afrika
Gwamnan Gombe Ya Ƙara Tallafin N148.76bn Domin Aiwatar da Sabon Tsarin Albashi A Jami’ar Gombe Afrika
An Bude Makarantu A Najeriya Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jihar Ekiti Ta Aiwatar Da Dokar Haraji Najeriya
  • APC Ta Ayana Tsohon Gwamnan Bauchi M.A Abubakar A Matsayin Dan Takarar Gwamna Afrika
  • ‘Yan Sanda A Jihar Gombe Sun Karyata Kona Gidan Nafiu Bala Afrika
  • Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Tura Sojoji Benin Labarai
  • Za’a Gurfanar Da Sojojin Da Ake Zargi Da Yunkurin Juyin Mulki Najeriya
  • Dusar Kankara Ta Hana Jirage Tashi A Birnin Paris Labarai
  • Malami: Gwamnatin APC Ta Gaza – “Yan-Kasa Kuwa Na Da Katin Zabe” Labarai
  • Kasar Aljeriya Ta Soke Yarjejeniyar Jirgin Sama Tsakaninta Da Daular Larabawa Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.