Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Sanatan Nasarawa Ta Arewa Ya Rasu A Kasar India
Published: January 2, 2026 at 12:54 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 2, 2026

Sanata Godiya Akwashiki, mai wakiltar Nasarawa ta Arewa, ya rasu yana da shekaru 52 a wani asibiti da ke ƙasar Indiya.

Rahotanni sun ce ya dade yana fama da rashin lafiya, kuma yana karɓar magani a Indiya kafin rasuwarsa.

Marigayi Akwashiki, wanda aka haife shi a ranar 3 ga Agusta, 1973, a Angba Iggah da ke ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon, ya taɓa rike mukamin shugaban masu rinjaye da mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, kafin daga bisani ya zama Sanata a shekarar 2019 karkashin jam’iyyar APC kuma an sake zaɓensa a 2023 karkashin jam’iyyar SDP.

Wani babban mataimaki ga marigayin Sanata, Ajegena Likita Ibrahim, ya tabbatar da rasuwar inda ya bayyana mutuwarsa a matsayin “babban rashi”.

Ibrahim ya shaida wa Daily Trust cewa suna ci gaba da tuntuba da ‘yan uwa a Indiya, amma har yanzu ba a fara shirye-shiryen dawo da gawar Sanata Akwashiki zuwa Najeriya domin jana’iza ba.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Kotu Ta Bada Belin Kwamishinan Kudin Jihar Bauchi
Next Post: Gwamnan Jihar Filato Ya Karbi Katin APC

Karin Labarai Masu Alaka

An Samu Nasarar Karbo Karin Yara 130 Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Amurka Ta Nuna Damuwa Kan Matsalar ‘Yan Gudun Hijira A Najeriya Najeriya
UNICEF Ta Tallafawa Jihar Bauchi Da Babura Afrika
Rikicin Aure: Albani Agege Ya Zargi Sheikh Gumi Da Boye Matarsa ‘Yar Morocco Afrika
Sojin Saman Najeriya Sun Lalata Sansanonin ‘Yan Ta’adda Afrika
Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Matasa Sun Sayawa Ferfesa Pantami Fom Din Takarar Gwamnan Gombe Afrika
  • Gombe Ta Ƙaddamar da Allurar Rigakafin HIV Ta LEN PrEP Afrika
  • An Kama Tsohon Jakadan Birtaniya A Amurka Peter Mandelson Amurka
  • Najeriya Da Dubai Zasu Karbi Bakoncin Taron Zuba Hannayen Jari Najeriya
  • Kenya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kasar Rasha Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya kori Wasu Hadimansa Bisa Cin Zarafin Kansila Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.