Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamna Abba Ya Gana Da Kwankwaso Kamun Ganawarsa Da Tinubu
Published: January 11, 2026 at 1:50 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 11, 2026

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gudanar da wata ganawar sirri da jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa da ke Miller Road, Kano, gabanin tafiyarsa zuwa ƙasar Faransa domin ganawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta gudana ne a daren Talata, 6 ga Janairu, 2026. Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnan ya isa gidan Kwankwaso da tsakar dare, cikin wata mota mai duhu.

Majiyoyi sun ce tattaunawar ta ɗauki sama da awa guda, amma bayanai sun nuna cewa gwamnan bai samu nasarar shawo kan Sanata Kwankwaso ba domin ya bi shi zuwa jam’iyyar APC, kamar yadda ake zargin akwai matsin lamba daga wasu manyan mutane.

Bayan kammala ganawar, washe gari, Sanata Kwankwaso ya yi jawabi ga magoya bayansa a gidansa, inda ya jaddada cewa ba shi da “farashi” a siyasa kuma yace cin amana ba abu ne mai kyau ba, yana mai nuni da matsalolin tsaro da tattalin arziki da ke rage farin jinin jam’iyyar APC a idon jama’a.

“Wasu na cewa a Nijeriya kowa na da farashi. Idan kana neman wanda ba shi da farashi, ka zo wurin Rabiu Kwankwaso,” in ji shi.

Rahoton ya ce shirin gwamnan na sauya sheƙa zuwa APC ya fuskanci cikas bayan shugabannin jam’iyyar sun lura da martanin jama’ar Kano, Duk da cewa wasu ‘yan majalisar dokoki na NNPP a matakin jiha da ƙasa, da kuma wasu shugabannin ƙananan hukumomi, na shirin sauya sheƙa tare da gwamnan, mafi yawan magoya bayan NNPP a jihar sun ci gaba da nuna cikakken goyon baya ga Kwankwaso.

Wata majiya ta bayyana cewa shugabannin APC na sa ido sosai kan halin da ake ciki a Kano, inda magoya bayan Kwankwasiyya ke nuna karara cewa suna tare da Kwankwaso.

Majiyar ta ce idan gwamnan ya shiga APC, akwai yiwuwar ɗan takarar da Kwankwaso ya goyi baya ya samu ƙuri’u masu yawa sakamakon ramuwar gayya.

Majiyoyi sun kuma ce Shugaban kasa na ci gaba da yunƙurin ganin Kwankwaso ya shiga APC, abin da ya sa ake neman shawo kansa ta hanyoyi daban-daban.

Rahoton ya ƙara da cewa ana sa ran gwamnan zai gabatar wa Shugaban kasa cikakken bayani kan sakamakon ganawarsa da Kwankwaso, tare da tsara matakan tafiyar da al’amuran jam’iyya idan ya yanke shawarar sauya sheƙa.

A halin yanzu, manyan shugabannin APC a Kano, ciki har da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin, shugaban jam’iyyar APC na jiha Abdullahi Abbas, da Nasiru Gawuna da Murtala Garo, sun dawo ƙasar nan bayan hutun ƙarshen shekara da aikin Umrah.

Ana sa ran Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sanar da matsayinsa kan batun sauya sheƙa ne bayan kammala shawarwari da shugabannin APC a jihar.

Siyasa

Post navigation

Previous Post: Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu
Next Post: Habasha Tafara Gina Filin Jirgin Sama Mafi Girma A Afirka

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Tinubu Ya Shiga Takara Wa’adi Na Biyu Afrika
Shugaban Kasar Uganda Yana Kokarin Mayar Da Mulkin Kasar Na Gado Labarai
Gwamnatin Tinubu Ta Warware Basussukan Fansho Na Shekaru 18 Afrika
PDP Ta Tsayar da Goodluck Jonathan Takarar Shugaban Kasa Afrika
Zaben Osun 2026: Darasi Ga APC, Gargadi Ga ADC, Nasara Ga Adeleke Afrika
Sanata Sa’idu Alkali Ya Kaurace Wa Zaben Fidda Gwani Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Morocco Ta Kwashe ‘Yan Kasar Daga Sassan Ambaliyar Ruwa Afrika
  • Tawagar IMF Tana Kasar Kenya Domin Tattauna Bada Lamuni Labarai
  • Take Hakkin Dan Adam Zai Haifar Da Juyin Juya Hali A Najeriya Najeriya
  • Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi A Edo Afrika
  • Majalisar Tarayya Ta Amince Da Gyara Dokar Kasafin Kudi Labarai
  • Kungiyar Kiristoci Ta Wanke Gwamnan Bauchi Daga Zargin Ta’addanci Labarai
  • Gabannin Harin Amurka Da Isra’ila Iran Farisa Ta Shirya Nata Afrika
  • Jami’an Tsaro A Jihar Borno Sun Kama ‘Yan Bindiga Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.