Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Habasha Tafara Gina Filin Jirgin Sama Mafi Girma A Afirka
Published: January 11, 2026 at 1:57 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 12, 2026

Firaministan Ethiopia, Abiy Ahmed, ya ce ƙasar ta fara gina abin da zai zama filin jirgin sama mafi girma a nahiyar Afirka.

A wani sakon da ya fitar a kafafen sada zumunta ranar Asabar, firaministan ya ce filin jirgin saman, mai suna Bishoftu International Airport (BIA), za a gina shi a garin Bishoftu a Ethiopia kuma za a kammala aikin a shekarar 2030.

“Domin ci gaba da haɓakar sufurin jiragen sama a Habasha da kuma faɗaɗa cibiyar sadarwar duniya ta Ethiopian Airlines, ana gina wani babban tashar jiragen sama (mega hub) tare da Filin Jirgin Sama na Addis Ababa Bole International Airport, wanda ke kusa da iyakar damar saukar fasinjoji miliyan 25 a kowace shekara,” in ji sanarwar.

“Bishoftu International Airport (BIA) zai zama babban aikin gina filin jirgin sama mafi girma a tarihin Afirka,” in ji shi.

Firaministan ya ce wannan shiri ya yi daidai da sauye-sauyen tattalin arziki na ƙasa, shirin masana’antu, da kuma tsarin dogon lokaci na harkar sufurin jiragen sama a Habasha.

Afrika, Labarai

Post navigation

Previous Post: Gwamna Abba Ya Gana Da Kwankwaso Kamun Ganawarsa Da Tinubu
Next Post: Tinubu: Mun Ware Biliyan 42 Don Inganta Lafiyar ‘Yan-Kasa

Karin Labarai Masu Alaka

Hamas Ta Kwance Damara Afrika
Tantance Gaskiyar Bayanai Shi Ne Ginshiƙin Aikin Jarida Mai Nagarta – Abdulaziz Afrika
Ministan Sufurin Najeriya Ya Ajiye Mukaminsa Domin Takarar Gwamna Afrika
Bayan Rikicin Manoma Da Makiyaya, Kwamitin White Paper Ya Ziyarci Bojude Da Kwami Afrika
Kasar Amurka Tabada Tabbacin Bawa Ukraine Tsaron Shekarun 15 Amurka
Shugaba Trump Yace Amurka Da Iran Suna Cigaba Da Tattaunawa Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Fiorentina Ta Yi Tayin Farko Ga Manchester United Kan Zirkzee Wasanni
  • Jana’izar Jagoran Ƙolin Iran Ta Kawo Tsauraran Matakan Tsaro A Tehran Afrika
  • Wani Alkali A Amurka Ya Kalubalanci Gwamnatin Kasar Afrika
  • Gwamnonin Arewa Maso Yammacin Najeriya Sun Halarci Taron Inganta Makashi A Birnin Landan Afrika
  • Burkina Faso Ta Sako Jami’an Rundunar Sojin Saman Najeriya 11 Da Aka Tsare Tsaro
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamna Bala Kauran Bauchi Ya Koma Jam’iyar APM Afrika
  • Ga Dukkan Alamu Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Bai Kare Ba Sauran Duniya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.