Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Shugaba Trump Ya Hana Kaiwa Cuba Man Fetur Daga Venezuela
Published: January 12, 2026 at 9:15 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ranar lahadi shugaba Donald Trump na Amurka yace babu man fetur ko sisin kwabo na Venezuela da zai sake zuwa Cuba, yana mai cewa ya kamata shugabannin kwaminis na kasar su nemi kulla yarjejeniya da Amurka kafin lokaci ya kure.

Kasar Cuba tana samun mafi yawan man fetur dinta daga Venezuela, amma babu jirgin mai ko guda daya da ya tashi zuwa Cuba daga can tun bayan da sojojin Amurka suka damko shugaba Nicolas Maduro.

Shugaba Miguel Diaz-Canel na Cuba yayi watsi da barazanar da shugaba Trump yayi a kafofin sada zumunci, yana mai cewa ai Amurka ba ta da hurumin sanya Cuba ta kulla wata yarjejeniya.

Diaz-Canel ya fada a shafin X cewa Cuba, kasa ce ‘yantacciya, mai cin gashin kai, kuma babu wani mahalukin da zai fada mata ga abinda zata yi.

Yace Cuba ba ta kai hari, amma Amurka ta yi shekaru 66 tana kai mata farmaki, yana mai fadin cewa a shirye suke su ci gaba da kare kasarsu.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Masar Tayi Yarjejeniyar Makamashi Da Kasashen Norway Da China
Next Post: Barcelona Ta Lashe Kofin Spanish Super Cup 

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Zata Aika Jiragen Yaki Biyu Gabas Ta Tsakiya Amurka
Amurka Ta Jefa Makamin Tomahawk A Makarantar Yara Mata Afrika
Dan Ra’ayin Mazan Jiya Leo Brent Zai Kyautata Alakar Afirka Ta Kudu Da Amurka Afrika
Akwai Bukatar Nazari Game Da Dangantakar Iran Da Kasashen Gulf Amurka
Za A Cigaba Da Tattaunawa Domin Kawo Karshen Yakin Gabas Ta Tsakiya Amurka
Shugaba Trump Yace Bazai Bari Iran Ta Mallaki Nukiliya Ba Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Da Alamu Ronaldo Zai Buga Dukkan Wasanni Da Gasar Kofin Duniya A 2026 Wasanni
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Gwamnatin Gombe Ta Aza Tubalin Gina Sakatariyar Gundumomin Cigaba (LCDAs) Labarai
  • ‘Yan Sanda Sunce Mutum Daya Ne Yakai Hare-Haren Jami’ar Brown Da Kuma Na MIT Boston Amurka
  • Amurka Tayi Barazanar Rage Tallafinta Wa Sudan Ta Kudu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mutane Biyu Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Da Ya Rutsa Da Antothy Joshua Najeriya
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya Rusa Majalisar Zantaswa ta Jihar Gombe Labarai
  • APC Ta Sauya Jerin ‘Yan Takararta Bayan Nazarin Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Fidda Gwani Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.