A yayin da aka kusa cika shekaru uku cif da barkewar yaki a kasar Sudan, an ci gaba da kokarin kawo zaman lafiya ranar laraba a birnin al-Qahira, inda Masar da Majalisar Dinkin Duniya suka yi kira ga sassan dake yakar juna da su yarda da tsagaita wuta na jinkai a fadin kasar.
Ministan harkokin wajen Masar, Badr Abdelatty ya shaidawa ‘yan jarida cewa kasarsa ba zata yarda kasar Sudan ko cibiyoyinta su rushe ba, kuma ba zata amince da duk wani yunkurin gurgunta hadin kanta ko rarraba yankunanta ba.
Abdelatty ya fada a taron ‘yan jarida na hadin guiwa da jakada na musamman na sakatare janar din MDD a Sudan, Ramtane Lamamra, cewa Masar ba zata nade hannu ba, kuma zata dauki dukkan matakan da suka kamata na tabbatar da ci gaba da hadin kan Sudan.


