Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Tattalin Arzikin Najeriya Ya Farfardo Bisa Samun Wasu Sauye Sauye
Published: January 15, 2026 at 9:05 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Najeriya ta shiga rukuni na karfafa ci gaba da ta samu ta fuskar tattalin arziki, bayan sauye sauye na shekaru biyu da gwamnatin kasar ta kaddamar, wadanda suka taimaka wajen tsaida hauhawar farashin kayayyaki, ya kawo daidaito kan darajar kudi, wadanda suka karfafawa masu zuba jari guiwa, kamar yadda ministan kudi Wale Edun ya fada a ranar Alhamis.

Tunda ya kama mulki a shekara ta 2023, shugaba Tinubu ya bullo da shirye shirye masu karfi na sauya fasalin tattalin arzikin kasar da aka dade sosai ba’a ga irinsu ba, da suka hada da janye tallafin man fetur, ya rage darajar kudin kasar har sau biyu, da kuma sauya dokar haraji da zummar bunkasa kudaden shiga ga gwamnati.

Matakan sun kawo matsanancin tsadar rayuwa da aka jima ba’a ga irinsa ba, amma suka inganta alkaluman tattalin arziki, sai dai kuma manyan kungiyoyin kwadagon  kasar sunce matakan sun jefa membobin su cikin wani mawuyacin halin rayuwa, inda hauhawar farashin kayayyaki ya durkusar da ma’aikata saboda, albashin su baya biyan bukata.

Ministan kudi Wale Edun, yace Najeriya ta doshi tudun mun tsira, bayan fadi tashin da tattalin arzikin kasar ya shiga sakamakon janye tallafin man fetur da gyaran fuska ga tafarkin canjin kudin kasar.

Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Yau Shekaru 60 Da Kisan Gilla Ga Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato
Next Post: Ghana Tayi Watsi Da Yarjejeniya Akan Hakar Ma’adanai

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Tinubu Ya Isa Legas Domin Hutun Karshen Shekara Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jama’a A Yankin Gulf Sun Bukaci Dakatar Da Hare Hare Daga Washington Afrika
Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Ya Bar PDP Ya Koma APC Labarai
Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina Labarai
Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka
Jami’ar ABU Zaria Ta Karbi Kudade Naira Bilyan 1.3 Daga Shirin Nelfund Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Akwai Nasara A Tattaunawar Da Akeyi Tsakanin Iran Da Amurka Afrika
  • Akwai Bukatar Bincikar Umurnin Da Sakataren Tsaro Pete Ya Bada Amurka
  • Jirgin Sojojin Ruwa Yayi Gobara A Cross River Najeriya
  • Kasar Congo Ta Dau Alwashin Bin Tsari Wajen Rarraba Ma’adanai Afrika
  • Fiye Da Mutane 200 Sun Rasa Rayukansu A Wajen Hakar Ma’adanai Labarai
  • Atiku Ya Bukaci Hadin Kan ‘Yan Adawa Domin Kawo Sauyi A Najeriya Afrika
  • Babban Sakataren MDD Yayi Allah Wadai Da Matakin Soja A Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Bankin Duniya Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Afirka Da Yankin Sahara Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.