Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani Afrika
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi Afrika
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Afrika
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika

CAF Ta Hukunta Samuel Eto’o AFCON 2025
Published: January 16, 2026 at 8:26 AM | By: Bala Hassan

An dakatar da tsohon tauraron kwallon kafa na Kamaru Samuel Eto’o na wasanni hudu tare da cin tararsa dala $20,000 (£14,960) bayan kwamitin ladabtarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (Caf) ya same shi da laifin rashin da’a.

Sanarwar Caf ta ce Eto’o, wanda yanzu shine shugaban hukumar kwallon kafa ta kasarsa Kamaru (Fecafoot), ya karya ka’idojinta na wasanni a lokacin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2025 tsakanin Kamaru da Morocco.

An ruwaito cewa tsohon dan wasan gaban Barcelona da Inter Milan ya nuna fushinsa kan wasu daga cikin shawarwarin da jami’an suka yanke yayin da Indomitable Lions ta sha kashi 2-0 a hannun masu masaukin baki Ƙasar Moroko.

Shugaban Caf Patrice Motsepe, wanda shi ma ya halarci filin wasa da ke Rabat, ya shaida faruwar abun inda ya nuna takaicin sa ga me da Eto’o.

A ranar Litinin hukumar gudanarwa ta nahiyar ta sanar da fara bincike kan “tashin hankali da kuma halayyar da ba a yarda da ita ba ta wasu ‘yan wasa da jami’ai” a wasannin ƙungiyoyi takwas na gasar ta AFCON.

A martanin da ta mayar, hukumar kwallon kafa ta Kamaru Fecafoot ta yi watsi da matakin na Caf, inda ta bayyana tsarin amatsayin abun shakku game da buƙatan shari’a mai adalci”.

Sannan Fecafoot ta nuna goyon bayanta ga shugabanta a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, yayin da ta nuna cewa Eto’o zai daukaka kara kan hukuncin.

Tun bayan da ya hau kan mukaminsa a shekarar 2021, an lalata tasirin Eto’o a matsayin gwarzon wasan saboda wasu hayaniya da ke da alaka da badakala da matsaniya.

Inda ya fuskanci zarge-zargen rashin da’a da rashin kyakkyawan shugabanci, wasu masu ruwa da tsaki a kwallon kafa suma ke korafin manyan kura-kurai a cikin Fecafoot.

A yayin tantance ‘yan wasa da zasu wakilci Ƙasar Kamaru a gasar cin kofin kasashen Afirka da ke guda na a Moroko an zargi Eto’o da sanya baki wajan kawo sunayen wadda ya ke so yayin da ya ceri wadda ake ganin basa shiri irin su maitsaron ragar Manchester United Andrew Onana, da Vincent Abubakar.

Sai dai Eto’o ya sha musanta irin wadannan zarge-zargen, yana mai bayyana nasarorin da aka samu a matsayin shugaban Hukumar.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Trump Ta Karawa Iran Wasu Takunkumai
Next Post: Dan Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Atiku Abubakar Ya Shiga Jam’iyyar APC

Karin Labarai Masu Alaka

An Kaiwa Sojojin Ghana Hari Da Makami Mai Linzami Afrika
Kenya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kasar Rasha Afrika
Hukumar Zaben Najeriya Ta Sanar Da Ranar Zaben Shugaban Kasa Labarai
NAHCON Ta Fitar Da Jadawalin Hajjin Bana 2027 Afrika
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Masu Zuba Jari A Birnin Paris Afrika
Shugaba Trump Yace Amurka Zata Janye Yaki Da Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sanarwar MDD Ya Nuna Aniyar Mayakan RSF Na Kisan Kare Dangi Afrika
  • Hukumar IMF Tana Naziri Domin Kara Bada Lamuni Ga Kasar Zambiya Afrika
  • Kamfanin Hakar Ma’adanai Na Kasar Kanada Ya Cigaban Da Aikinsa Labarai
  • Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka
  • Amurka Ta Kakaba Takunkumi Ga Kwamandojin Yakin Kasar Sudan Sauran Duniya
  • Dogarawan Ruwa Na Amurka Suna Yunkurin Shiga Wani jirgin Dakon Mai Da Aka Allakan Ta Da Venezuela Labarai
  • An Kashe Mutane 169 A Wani Harin Sudan Ta Kudu Afrika
  • Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso Ya Fice Daga NNPP Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.