Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Suvr Jahun: Ya Kamata Obasanjo Ya Bar Al’umar Ƙasa Su Fito Da Wadda Suke So 2027
Published: January 21, 2026 at 9:00 AM | By: Bala Hassan

An ja hankalin tsohon Shugaban Kasar Najeriya Olushegun Obasanjo kan wasu kalaman kiyayya da yake yi wa Atiku Abubakar

Suvr. Lawal Jahun Chiroman Galadiman Bauchi tsohon Malamin Kwalejin kimiya da fasaha na gwamnatin tarayyar Najeriya dake Bauchi shine yayi wannan kira ga Obasanjo, a wata hira da yayi da GTA Hausa.

Lawal yace Obasanjo yanzu a Najeriya shi uba ne saboda haka kowa nasane bai da ce da wasu kalamai na nuna cewa Atiku Abubakar bai cancanci zama Shugaban ƙasa ba.

Mun san cewa Atiku yayi mataimaki wa Obasanjo na tsawon shekaru takwas duk da cewa an san sun kare dutse a hannun riga amman Atiku ya taimaki Obasanjo a lokacin da ya ke niman tazarce, shi ya shawo kan Gwamnoni musan na arewa yace suyi hakuri su sake zaban Obasanjo karo na biyu

An sani cewar duk shugaba yana da yadda za’a yaba masa bisa wasu ayyukan cigaba da ya kawo a kwai kuma yadda ya gaza saboda shi dan adam ne tara yake bai cika goma ba.

A lokacin Obasanjo cigaba da aka samu a shi ne bangaren tsaro da kuma yaki da yunwa, wannan kowa yasani amman a inda yagaza shine ya halarta wa gwamnonin jihohi su karbi kudin kananan Hukumomin wadda ya jawo kananan Hukumomin suka fita hayyacinsu a yanzu haka.

Matsalolin da aka samu tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku da Obasanjo ai shi Atiku yayi tattaki har zuwa gidan gonan Obasanjo domin su dai dai ta amman Obasanjo yaki ” Inji Suvr Lawal.

Amman abunda muka fahinta shine Obasanjo yana kin Atiku ne saboda yana tsoron kar ya tona masa wani asiri tunda sunyi aiki tare ya san wasu sirrinsa, ko kuma ya na tsoron kar ya rama abunda ya masa duk da bama son a yi mulki na ramukon gayya.

Saboda haka idan Obasanjo bazai goyi bayan Atiku ba to ya bari al’umar ƙasa su zabi wadda suke so domin su za’a mulka.

Lawal ya kara da cewa yanzu a Najeriya babu wani kamar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar in dai batun siyasa ne haka kuma a jihar Bauchi Baba kamar Air vice Marshal Sadiq Baba Abubakar ritaya.

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/01/SUVR-LAWAL-JAHUN.mp3
Najeriya

Post navigation

Previous Post: Menene Illar Yada Labaran Karya A Kafofin Sada Zumunta Na Zamani
Next Post: Sojojin Najeriya Sun Kwato Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dawo Da Dokar Zirga Zirgar Babura A Jihar Gombe Afrika
Gwamnatin Tarayyar Najeriya Zata Raba Taki Ga Manoma Afrika
An Kusa Kawo Karshen Matsalolin Tsaro A Jihar Filato Afrika
Shugaba Tinubu Ya Shiga Takara Wa’adi Na Biyu Afrika
Tinubu Ya Bayyana ‘Yan Bindiga Da Cewa Ruwa Yakarewa Dan Kada Afrika
NAHCON Tafara Shirye-Shiryen Aikin Hajjin 2026 Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Najeriya Na Shirin Yin Zamiya Don Biyan Bashi Labarai
  • Shugaban Ƙasar China Zai Karbi Bakwancin Shugaban Koriya Ta Kudu Afrika
  • Anfara Samun Sakamakon Wucin Gadi a Kasar Guinea Conakry Labarai
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika
  • ‘Yan Bindiga A Mali Sun Kashe Direbobin Manyan Motoci Afrika
  • Shugaba Trump Yace Tehran Tana Neman Kulla Alaka Da Washington Amurka
  • Tattalin Arzikin Najeriya Ya Farfardo Bisa Samun Wasu Sauye Sauye Labarai
  • Shirin Ga Fili GA Doki Shirye-Shirye
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.