Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani Afrika
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi Afrika
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Afrika
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika

Za’a Gurfanar Da Sojojin Da Ake Zargi Da Yunkurin Juyin Mulki
Published: January 26, 2026 at 8:38 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 28, 2026

Binciken da rundunar sojin Nigeria ta yi ya gano akwai yiwuwar cewa wasu dakarun ta 16 da aka kama shekarar da ta gabata saboda aikata laifi, suna shirin kifar da gwamnati ne ta hanyar juyin mulki, kuma zasu fuskanci shari’a, a cewar wani jawabi da ya fito daga babban ofishin tsaro na kasa a ranar litinin.

Jawabin ya ce binciken da aka yi ya binciko sahihan abubuwa a kan da yawa daga cikin sojojin, ciki har da zargin shirin hambarar da gwamnati, amma bai bada bayanin yadda shirin nasu yake ba, da ko sojoji nawa daga cikin 16 ne ke da hannu ciki ba.

Mai magana da yawun hukumar tsaro major janar Samaila Uba, ya ce an tsare Jami’an sojojin a watan Octobar bara, wadanda kuma ake tuhumar su da laifin yunkurin Juyin mulki yanzu za’a tsayar da su gaban alkalin kotun soja. Ya kara da cewa, idan an kama su da laifi, zasu fuskanci hukuncin kisa.

A watan Octoba na shekarar da ta wuce ne, Shugaba Bola Tinubu ya sauya sojoji masu rike da manyan mukamai da wasu, a yunkurin sa na karfafa matakan tsaro, yayin da kasar ke fuskantar barazana daga kungiyoyin ‘yan ta’adda da dama.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Abba Kabir Yusuf Ya Koma Jam’iyar APC
Next Post: Kungiyar ‘Yan Ta’adda Masu Alaka Da ISIS Sun Kashe Mutane A Congo

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina Labarai
Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Dawo Da Kudaden Ma’aikata Afrika
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Jama’ar Arewa Maso Gabas Afrika
Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci Afrika
Kungiyoyin Fararen Hula A Gombe Sun Bukaci A Bawa Mata Jagoranci Afrika
An Gudanar da Taron Kwana Biyu kan Tsarin Sa Ido da Tantance Ayyukan AGILE a Jihar Gombe  Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Sanda A Jihar Gombe Sun Karyata Kona Gidan Nafiu Bala Afrika
  • Jami’an Askarawa A Zamfara Sun Kama Na’urorin Fashewa Da Makudan Kuɗaɗe Afrika
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Asabar 11.15.2025 Rediyo
  • Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Aika Sammaci Dr. Yusuf Baba-Ahmed Labarai
  • Guinea An Zabi Madugun Sojojin Da Suka yi Juyin Mulki Mamady A Shugaban Ƙasar, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Majalisar Wakilai Ta Rikon Kwaryar Nijar Ta Gudanar Da Zama Karo Na Biyu Afrika
  • Gwamnatin Kano: Zamu Kara Daukar Malamai Domin Inganta Ilimi Najeriya
  • Ba Shakka Najeriya Zata Iya Shiga Gasar Harbi Ta Duniya Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.