Hukumar ladabtarwa ta CAF ta kakabawa hukumar kwallon kafa ta Senegal FSF, da hukumar kwallon ta Moroko takunkumi.
Hukumar ladabtarwa ta (“CAF”) ta sanya takunkumi kan Senegal da Moroko da wasu ‘yan wasa da jami’ai game da abubuwan da suka faru a lokacin gasar cin kofin Afirka na CAF na Moroko 2025, wanda ya keta ka’idojin CAF.
Hukumar ladabtarwa ta CAF ta dauki matakai kamar haka:
Game da Hukumar Kwallon Kafa ta Ƙasar Senegal (FSF), Hukumar Ladabtarwa ta CAF ta yanke shawarar dakatar da Mr Pape Bouna Thiaw, Babban Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Senegal, na wasanni biyar (5) Wacce CAF ta shirya saboda rashin da’a da a wasan karshe wanda ya saba wa ka’idojin dokar CAF da kuma kawo rashin mutunta wasan an kuma ci Pape Bouna Thiaw tarar dalar Amurka 100,000.
Bayan haka CAF ta dakatar da dan wasan Senegal, Iliman Cheikh Baroy Ndiaye na wasanni biyu (2) na CAF, saboda rashin da’arsa ga alkalin wasa, CAF ta dakatar da dan Senegal, Ismaila Sarr na wasanni biyu (2) na CAF shima saboda rashin da’a da ya yi wa alkalin wasa.
Ita ma hukumar kwallon kafa ta Ƙasar Senegal (FSF), an ci tararta dala 300,000 saboda rashin da’a da magoya bayanta, suka nuna a ranar wasan wanda ya karya ka’idojin CAF na yin wasa mai kyau da mutunci, da kuma karin tarar dala 300,000 saboda rashin da’a daga ‘yan wasansu da ma’aikatan horaswa wanda CAF ta bayyana shi a matsayin rashin mutunta wasan.
Akwai tarar ga (FSF), dala 15,000 saboda rashin da’a na kungiyarta ta Ƙasar, saboda biyar (5) cikin ‘yan wasanta sun sami gargadi.
A bangaren Hukumar Kwallon Kafa ta Ƙasar Moroko (FRMF), Hukumar Ladabtarwa ta CAF ta yanke shawarar
dakatar da dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Moroko, Achraf Hakimi na wasanni biyu (2) na hukumar CAF, tare da dakatar da wasa daya (1) na tsawon shekara daya (1) daga ranar da aka yanke wannan hukunci, saboda rashin da’a da ya yi a wasan, bayan haka CAF ta dakatar da dan wasan kungiyar kwallon kafa na Moroko Ismaël Saibari wasanni uku (3) na hukumar CAF shima saboda rashin da’arsa an kuma ci Ismaël Saibari tarar dala 100,000.
CAF ta kuma ci tarar hukumar kwallon kafa ta Ƙasar Moroko (FRMF) dala 200,000, saboda rashin da’ar ‘yan wasan a filin wasa a lokacin wasan karshe na kofin kasashen Afirka AFCON 2025.
Da kuma karin tarar dala 100,000 saboda rashin da’a na ‘yan wasanta da ma’aikatan horaswa, waɗanda suka mamaye duba VAR suka kuma hana aikin alkalin wasa, wanda ya saɓa wa ƙa’idodin yin wasa sashe na 82 da 83 na Dokar Ladabtarwa ta CAF.
A kwai kuma tarar da aka ci Hukumar Kwallon Kafa ta Moroko (FRMF) dala 15,000 saboda amfani da na’urorin laser da magoya bayanta suka yi a lokacin wasan aikata haka laifine.
Dangane da korafin kan Hukumar Kwallon Kafa ta Moroko (FRMF) ta shigar kan zargin keta dokoki daga Hukumar Kwallon Kafa ta Senegal (FSF) inda ta bukace a kwace kofin bisa sashe na 82 da 84 na Dokokin Gasar Cin Kofin Afirka kuwa
hukumar Ladabtarwa ta CAF ta yi watsi da wannan korafin da Hukumar Kwallon Kafa Moroko (FRMF) ta shigar kan Senegal (FSF).


