Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Jakadan Amurka A Poland Ya Yanke Hulda Da Kakakin Majalisar Kasar
Published: February 6, 2026 at 11:22 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jakadan Amurka a Poland, ya yanke hulda da kakakin majalisar kasar a ranar Alhamis, yana zargin kakakin majalisar cewa ya zagi shugaban Amurka Donald Trump, bayanda ya soki manufofin gwamnatin shugaban na Amurka, da kuma kin goyon bayan a baiwa Trump Lambar yabo ta Nobel.

Wakilan gwamnatin hadin guiwa a Poland suna tsaka mai wuya a kokarin su na lallaba dangantakar su da shugaba Trump a gefe daya kuma su masu ra’ayin turai ne.

Musayar zazzafar kalamai a shafukan dandalin sada zumunci na X, ya jawo PM kasar Poland Donald Tusk, wanda yace “Ambasada Rose, kawaye suna mutunta juna ne, ba yi wa juna laccha ba, Akalla dai mu a Poland haka muka fahimci abunda kawance yake nufi.”

Kakakin majalisar dokokin Poland, ya fada ranar Litinin cewa, ba zai goyi bayan kudurin da kakakin majaisar dokokin Amurka Mike Johnson, dana Isra’ila suka gabatar na neman hada kan shugabannin majalisun kasashe su goyi bayan yakin neman a baiwa shugaba Donald Trump lambar yabo ta Nobel.

Labarai

Post navigation

Previous Post: China Ta Kori Wakilan Majalisar Dokoki Uku A Kasar
Next Post: ‘Yan Jarida Sunyi Mummunan Hatsari A Bauchi

Karin Labarai Masu Alaka

Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Yayi Ajalin ‘Yan Ghana 50 Afrika
APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika
Hukumar Zabe A Kasar Honduras Ta Sanar Da Nasry Asfura A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Ƙasa Afrika
Shugaban Amurka Donald Trump Yace Amurka Zata Kai Babban Farmaki Iran Afrika
Osun: Adeleke Ya Doke Oyebamiji, Ya Ci Gaba Da Rike Kujerar Gwamna Afrika
‘Yan Bindiga A Mali Sun Kashe Direbobin Manyan Motoci Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sabuwar Shekarar Musulunci: Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Yi Kira Da A Yawaita Addu’o’i Da Haɗin Kai Afrika
  • Amurka Tana Cigaba Da Kare Jami’in Da Ya Kashe Ba Amurke Amurka
  • ‘Yan Bindiga A Mali Sun Kashe Direbobin Manyan Motoci Afrika
  • Kasar Gabon Ta Nemi Tallafin Asusun Bada Lamuni Na IMF Afrika
  • Shugaba Trump Ya Bukaci Kasar Iran Ta Mika Wuya Amurka
  • An Gudanar Da Taron Matasan Kasashe 6, Don Kawo Karshen Ta’addanci Wasanni
  • Za A Cigaba Da Tattaunawa Domin Kawo Karshen Yakin Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Jirgi Marar Matuka Yayi Luguden Wutan A Abu Dhabi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.