Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Ana Cigaba Da Yaki Tsakanin Amurka Da Isra’ila Da Kasar Iran
Published: March 4, 2026 at 2:49 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ana ci gaba da gwabza yaki, tun bayan da Amurka da Isra’ila suka kai wa kasar Iran hari, inda suka kashe shugaban ta Ayatollah Ali Khameni. Isra’ila na ci gaba da kai hari Tehran, babban birnin Iran da kuma Beirut, babban birnin Lebanon, inda itama Iran ta mai da martani wajen kai hare-hare sansanonin sojin Amurka dake gabas ta tsakiya, ta kuma rufe mashigin ruwa na Hormuz, inda jiragen dakon man fetur ke ratsawa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da yiwuwar sojin Amurka cewa zasu yiwa jiragen dakon man fetur dafifi don su samu wucewa ta hanyar mashigin ruwa na Hormuz. Ita kuma Iran ta dau alwashin harbo duk wani jirgi da ya wuce ta nan.

Kasuwannin hada-hadar hannun jari sun rikice, yayin da farashin danyen man fetur ya tashi sakamakon yakin.

A jiya Talata ne kuma aka samu sabanin ra’ayi game da dalilin da ya sa Amurka ta kaiwa Iran hari tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da kuma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio.

Trump ya ce ya umurci Isra’ila da ta kaiwa Iran hari saboda yana da yakinin Iran na da niyyar fara kawo musu hari. A nasa bangaren shi kuma Marco Rubio ya sha banban, inda ya shaidawa manema labarai ranar Litinin cewa Amurka ta kaiwa Iran hari ne saboda fargabar da ake yi na cewa Iran zata mai da martani game da shirin kaiwa Tehran hari da Isra’ila ta yi.

Ya ce mun san Isra’ila zata kai hari, kuma mun san cewa za’a mai da martani ta kai hari kan sojin Amurka, mun san idan bamu far musu ba zasu yi mana barna me yawa.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Dakarun Pakistan Da Afghanistan Sunyi Arrangama
Next Post: Kamfanin Mai Mallakar Saudiya Aramco Zai Sanja Hanyar Fitar Da Danyen Mai

Karin Labarai Masu Alaka

Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
Shugaban Kasar Madagascar Ya Kori Prime Minista Da ‘Yan Majalisa Afrika
Tinubu Ya Sayi Fom Din Takarar Shugaban Kasa Afrika
Sakataren Tsaron Amurka Yace Baza’a Bayyana Bidiyon Kai Hari Akan Jirgin Ruwa Ba Amurka
Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda Afrika
Majalisar Kwararrun Iran Ta Sanar Da Sabon Shugaban Addini Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kotu A Kasar Tunisiya Ta Daure Wani Babban Dan Kasuwa Da Wasu ‘Yan Majalisa Afrika
  • Ambaliyar Ruwa Yayi Ajalin Mutane A Nairobi Afrika
  • Wasu Mutane 15 Sun Rasa Rayukan Su A Gabashin Kwango Afrika
  • An Fara Azumin Watan Ramadan A Najeriya Da Sassan Duniya  Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ba Mamaki APC Ta Kafa Tarihi A Ranar Litinin Najeriya
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tallafa Wa ’Yan Sanda Da Motoci Afrika
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Talata 11.18.2025 Rediyo
  • Amurkawa Sun Nuna Bacin Rai Saboda Yawaita Kashe ‘Yan Kasar Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.