Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Farashin Danyen Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya
Published: March 6, 2026 at 5:07 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Farashin danyen mai ya tashi a kasuwannin duniya a ranar Alhamis, da kashi 3 cikin dari, inda aka yi cinikin gangar mai akan dala 84 da centi 32 na mai da ake kira Brent, yayinda wadda ake kira West Texas ya tashi kan dala 79 da centi 6 da tsakar ranar jiya agogon Amurka, yayinda yakin hadin guiwar Amurka da Isra’ila akan Iran ke kara tsanani, lamari da ya kassara jigilar mai daga gabas ta tsakiya.

An sami karin hare hare kan jiragen ruwa masu dakon mai a wuraren da suke yankin Gulf, rahotanni suka ce jiragen yaki da basu da matuka daga Iran sun kutsa Azerbaijan ranar Alhamis, mataki da yake barazana ga kara bazuwar yaki zuwa kasashe dake hakar mai a yankin.

Iran ta auna hari kan wani jirgin ruwa mai dakon mai dauke da tutar Bahamas, wadda yake tsaye a wata tasha a gabar Iraqi, haka nan wani jirgin ruwa ba nesa da gabar ruwan Kuwait ya fara kwasar ruwa, kuma har yana yoyon mai, bayan da ya fuskanci wani abun fashewa a tashar da yake.

An kaiwa jiragen ruwa 9 hari tun barkewar fada tsakin hadin guiwar Amurka da Isra’ila kan Iran a ranar Asabar data shige. Iran ta harba makamai masu linzami kan Isra’ila a ranar Alhamis, kuma jiragen yakin kasar maras matuka a wani kutse da suka yi a Azerbaijan ya jikkata mutum hudu, har aka ji Azerbaijan tana barazanar zata maida martani.

Kimanin jiragen ruwa dari biyu ne, dauke da mai da iskar gas, da masu dakon kaya ne suke tsaye a gabar ruwaye dake yankin Gulf ahalin yanzu, kamar yadda wani kiyasi da kamfanin dillancin labarai na Reuters yayi bisa la’akari da bayanai daga wata kunigya dake sa ido kan zirga zirga jiragen ruwa a duniya.

A cikin kalamansa na baya bayan nan shugaban Amurka Donald Trump, yace tilas ya tsoma baki wajen wadda zai gaji marigayi Shugaban addinin Iran, kuma yace ko kusa Amurka ba zata amince dan tsohon shugaban addinin Ayatollah Khameni ya gaji mahaifinsa ba.

Afrika, Amurka, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Majalisa A Kasar Somaliya Ta Amince Da Sauya Tsarin Mulkin Kasar
Next Post: Amurka Da Tarayyar Turai Sun Fidda Sanarwa

Karin Labarai Masu Alaka

Magoya Bayan Tijjaniyya Zasu Kauracewa Zabe Saboda Kama Sheikh Sani Khalifa Afrika
NAHCON Ta Kaddamar da Tawagar Malamai Afrika
Nnamdi Kanu Ya Nemi A Mayar Da Shi Abuja Daga Gidan Yarin Sokoto Labarai
Ruwan Sama Yayi Ajalin Daruruwan Mutane A Afirka Ta Kudu Afrika
Ambaliyar Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutum 13 A Malawi Labarai
Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Za’a Ninka Shekarun Kurkuku Ga Masu Aikata Luwadi A Senegal Afrika
  • Kasashen Cambvodia Da Thailand Sun Kulla Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsaro
  • Gwamnatin Kebbi Ta Samu Tankokin Yaki Tsaro
  • Shugabar Kungiyar Cinikayya Ta Duniya Ta Bukaci Kasashe Su Gyara Harkokin Cinikayya Afrika
  • Jagoran Adawar Uganda Bobi Wine Ya Fice Daga Kasar Afrika
  • ‘Yan Uwan Wadanda Aka Kashe Sunkai Kara Kotu Amurka
  • Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia Afrika
  • Gobara Ta Lalata Shaguna Da Gidajen Abinci A Gombe Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.