Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Kasar Ghana Zata Sauya Inda Take Kai Sarrafa Gwal
Published: March 6, 2026 at 10:09 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin kasar Ghana na shirin sauya shekar inda take aikewa da gwal dinta don sarrafa shi, idan aka ci gaba da samun tsaiko wajen tashin jiragen sama zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa, a cewar wasu majiyoyi biyu dake da masaniya kan abun, yayin da rikicin Iran ya bankado yadda Afirka take dogaro da Dubai a harkar gwal.

Ana aikewa da gwal kai tsaye zuwa Dubai, wadda babbar kasuwa ce dake cinikar da gwal din ga kasashen Switzerland, Honk Kong, da kuma India. Yau kwanaki 7 kenan da samun tsaiko wajen aika gwal din a dalilin harin da Amurka da Isra’ila suka kaiwa Iran, da ita kuma Iran din ta kai harin kan sansanin sojin Amurka a Gabas ta tsakiya, abinda ya jawo rufe tasoshin jiragen sama a Dubai.

Ita kuma Ghana, wadda ita ce kasar da tafi samar da gwal a Afirka, kuma ta 6 a duniya, Dubai ce ke sarrafa kusan kashi 80 cikin 100 na gwal din ta. Amma saboda yakin da ake tafkawa, ya rufe hanyar Dubai, Ghana ta shirya tsarin kai gwal din zuwa China ko India don sarrafawa.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 15 Da Wasu Fararen Hula A Benin
Next Post: An Kaiwa Sojojin Ghana Hari Da Makami Mai Linzami

Karin Labarai Masu Alaka

An Gargaɗi Mazauna Maiduguri Su Guji Yaɗa Labaran Ƙarya Afrika
Gwamna Ahmad Aliyu Na Jihar Sokoto Ya Gabatar Da Kasafin Fiye Da Naira Biliyan 700 Labarai
An Fara Dawo Da Alhazain Najeriya Gida Afrika
Mun Kwato Kimanin Naira Biliyan 40 Na Badakala A Tsawon Shekara Daya Labarai
Shugaba Trump Yace Zai Dakatar Da Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran Afrika
Shugaban Kasar Ghana Ya Soki Manufofin Gwamnatin Amurka Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jami’an Tsaron Pakistan Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Labarai
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Katsina Afrika
  • Kotu A Kasar Uganda Ta Bada Belin ‘Yar Gwagwarmaya Afrika
  • Kungiyar Kiristoci Ta Karyata Kubutar Da Mambobin Su A Kaduna Afrika
  • Allah Ya Yi Wa Sheikh Dahiru Bauchi Rasuwa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Canza Shugabannin Hukumar Hakar Ma’adanai A Congo Labarai
  • Masu Ruwa da Tsaki akan Lamurran Siyasa sun Fara Maida Martani akan Matakin da Ministan Labaran Nigeria da wayar da kan Jama,a Idris Malagi na korar Daya Daga cikin Ma,aikatansa Saboda dalilai na Siyasa. da tsakiayar ranar Wannan larabace dai Mataimakin na Musamman akan yada Labarai ga Minista Malagi Malam Rani,u Ibrahim ya fitar da Wata sanarwar cewa Ministan ya Dakatar da Daya Daga cikin Ma,aikatansa Mai Suna Sa,idu Enagi Saboda ya fitar da Wani bayani a Kafar yada Labarai na sada zumunta dake Nuna Ministan ya shirya tsaf Domin takarar Gwamnan Jihar Neja a 2027. Malam Sa,idu Etsu Tsohon Dantakarar Shugaban cin Jam,iyyar APC a Nigeria Yace Matakin da Ministan ya Dauka yayi Dai dai Domin yanzu lokaci baiyi ba..ceu.. Shima Dattijon Siyasa a Jihar Neja Alh.Awaisu Giwa Kuta Yace Matakin da Ministan Labaran ya Dauka yayi Dai dai Domin yanzu Jihar Neja zaman Makoki Ake na fotinar Yan ta,adda ba wai Batun Neman Mukamin Siyasa ba..ceu .in.. To Sai jigon Jam,iyyar PDP Mai Adawa a Nigeria Hon.Yahaya Ability Yace Akwai kuskure Babba da Ministan ya tabka a dai dai Wannan Zamani na Siyasa duk da cewa Jihar Nejan na cikin Yanayi na masifar Yanbindiga..ceu..in .. Azaben Shekara ta 2023 Malagi ya kara yayi Takara Gwamnan Jihar Neja a jam,iyyar APC inda Gwamna Umar Bago ya kadashi a zaben fidda Gwani.
    Martanin Wasu ‘Yan Najeriya Ga Ministan Labarai Bisa Korar Dadiminsa Najeriya
  • Gwamnatin Najeriya Ta Jaddada Aniyarta Ta Daƙile Yaɗuwar Makamai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.