Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Iran Ta Karyata Tattaunawa Da Washington
Published: March 24, 2026 at 4:33 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ranar Litinin, Iran ta musanta cewa ta gudanar da shawarwari da Washington, bayan da shugaba Donald Trump ya dakatar da barazanar da yayi na lalata tashoshin wutan lantarki na Iran, sakamakon abunda ya kira tattaunawa mai ma’ana, da wasu jami’an Iran wadanda bai bayyana ko su wanene bane.

Wani jami’i a turai yace kodashike babu wata tattaunawa ido da ido tsakanin kasashen biyu, kasashen Masar, da Pakistan, da wasu kasashen da suke yankin Gulf, suna kai sakonni tsakanin kasashen biyu. Wani jami’i a Pakistan da wata majiya sun gayawa kamfanin dilanciin labarai na Reuters cewa, sai tayiwu a gudanar da shawarwari kai tsaye na kawo karshen yaki tsakanin kasashen biyu cikin wannan mako a Islamabad.

Trump ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta da ake kira Truth Social cewa, Amurka da Iran sun gudanar da shawarwari cikakke mai ma’ana, na kawo karshen yakin baki daya a yankin gabas ta tsakiya.

A sakamakon haka ne yace, zai dakatar da barazanar da yayi na kai hari kan cibiyoyin wutan lantarkin Iran, wannan sanarwar ta sa Hannayen jari a kasuwannin duniya suka cira, yayinda farashin mai ya yayi kasa da dala dari akan ko wace gangar danyen mai.

Ahalinda ake ciki kuma, wata jaridar Amurka da ake kira Politico, ta bada labarin cewa Amurka tana auna kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammed Bagher Ghalibaf a zaman abokin hulda, ko kuma ta goyi bayansa a zaman shugaban kasar nan gaba, kamar yadda jaridar ta fada a jiya Litinin, inda ta ambaci jami’an Amurka biyu dangane da wannan batu.

Afrika, Amurka, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sarkin Gombe Yayin Hawan Tudun Wada
Next Post: Shugaban Kasar Ukraine Yace Rasha Tana Bawa Iran Bayanan Sirri

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar Iran Zata Kai Hare Haren Ramuwar Gayya Isra’ila Afrika
Kasar Netherland Ta Mayarwa Masar Mutum Mutumin Tarihi Afrika
Gwamnatin Tarayya Za Ta Sake Fasalin Shirin NYSC Afrika
An Garkame Wani Babban Soja A Kasar Australiya Afrika
Zargin Fitar Da Bayanan Masu Zabe A Najeriya Afrika
Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Tarayya Zata Fara Gwajin Shan Kwaya Kafun Daukar Aiki Kiwon Lafiya
  • Afirka Ta Kudu Ta Samu Rigakafin Cutar Boro Afrika
  • Wani Alkali A Kotun Amurka Ya Dakatar Da Kudurin Shugaba Trump Afrika
  • Hukumomin Taliban Sunce A Shirye Suke Domin Sulhu Afrika
  • Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Isra’ila Ta Cire Sunayen Wasu Mutane Biyu Cikin Wadanda Take Fako Afrika
  • Za’a Saka Tarihin Trump A Manhajar Makarantu Don Jajircewasa Da Kwazo Amurka
  • Fafaroma Leo Yayi Allah Wadai Bisa Karuwar Yake Yaken Gabas Ta Tsakiya Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.