Farashin mai ya ragu a jiya Laraba bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka za ta kawo ƙarshen yaƙin da take yi da Iran nan ba da jimawa ba.
Farashin Man Brent ya faɗi da dala $2.81, wato kashi 2.7%, inda ya tsaya a $101.16 kowace ganga, bayan ya taɓa sauka zuwa $98.35 a lokacin ciniki. Haka kuma, farashin ɗanyen Mai Amurka na West Texas Intermediate (WTI) na watan Mayu ya ragu da dala $1.26, kusan kashi 1.2%, zuwa $100.12 kowace ganga, daga ƙasa mafi ƙanƙanta na $96.50.
A ranar Talata, Trump ya nuna cewa Amurka na iya kawo ƙarshen yaƙin cikin makonni biyu zuwa uku ko da ba tare da wata yarjejeniya ba. Wannan furuci ya sa farashin mai ya sauka da sama da dala $3 kowace ganga a wancan lokacin ciniki.
Masu saka jari a kasuwa na hasashen cewa Trump ba zai bari tangardar samar da mai sakamakon yaƙin Gabas ta Tsakiya ta wuce tsakiyar watan Mayu ba, lokacin da buƙatar man fetur a Amurka ke kai kololuwa, kamar yadda masana na SEB suka bayyana.
Sunce, “Barazanar hauhawar farashin man fetur a Amurka, tasirin hakan ga ra’ayin masu saye, da kuma yiwuwar tasiri ga zaɓen tsakiyar wa’adi na watan Nuwamba, na sa tsawaita yaƙin zai zama mai tsada a siyasa.”
A ranar Litinin, farashin man fetur a Amurka ya haura dala $4 kowace galan a karon farko cikin sama da shekaru uku.


