Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

An Gudanar Da Tiyatar Ido Kyauta A Gombe
Published: May 2, 2026 at 7:35 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

An gudanar da wannan shirin ne ta hannun Hukumar Tara Haraji ta jihar Gombe, ƙarƙashin jagorancin shugabarta, Aisha Adamu, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Imkhahad Development Initiative.

Shirin na tsawon kwanaki uku, wanda aka yi daga ranar ɗaya zuwa uku ga watan Mayu, dubu biyu da ashirin da shida, ya gudana a ƙauyen Hina da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, inda akayi gwaje-gwaje, shawarwari, magunguna, tiyata da kuma tabarau na gani kyauta ga al’umma.

Da take jawabi a wajen buɗe shirin, Shugabar Hukumar, Aisha Adamu, ta jaddada muhimmancin danganta biyan haraji da ci gaban al’umma kai tsaye. Ta kuma yaba wa Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa goyon bayan da yake bayarwa, wanda ta ce shi ne ya ba da damar aiwatar da irin waɗannan shirye-shirye.

Ta kuma gode wa ƙungiyar Imkhahad Development Initiative, musamman shugabarta, Umulkairi Adamu, bisa jajircewarta wajen ayyukan jin ƙai da haɗin gwiwa domin magance matsalolin lafiyar idanu a yankunan da ba su da isasshen kulawa.

Shugabannin al’umma ma sun yaba da wannan shiri. Sarkin Yamaltu, Abubakar Aliyu, wanda Alhaji Isa Idris Tela, Hakimin Hina ya wakilta, ya bayyana shirin a matsayin mai muhimmanci kuma mai kawo sauyi, yana mai cewa ingantacciyar lafiyar idanu za ta ƙara yawan aiki da inganta rayuwar al’umma.

A nasa bangaren, Likitan da ya jagoranci shirin daga asibitin Shifa Eye Care, Dokta Lawali Mohammed Kumo, ya shawarci waɗanda suka amfana da su bi umarnin likitoci da kula da kansu bayan tiyata domin samun cikakken waraka.

Abin lura a yayin shirin shi ne, wasu daga cikin waɗanda suka zo ba sa gani sun koma gidajensu suna gani bayan an yi musu tiyata.

Masu amfana da shirin sun bayyana godiyarsu, suna mai cewa wannan taimako ya dawo musu da gani tare da ba su damar ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Shugabar Hukumar Tara Haraji ta Jihar Gombe ta ce shirin na ci gaba da zama hujja cewa yadda ake tara haraji yadda ya kamata na iya haifar da ayyukan ci gaba masu amfani, tare da ƙarfafa amincewar jama’a da kuma ƙara yawan biyan haraji da son rai.

Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Shugaba Tinubu Ya Tafi Kasar Faransa
Next Post: Tsohon Ma’aikacin VOA Saleh Shehu Ashaka Ya Rasu

Karin Labarai Masu Alaka

Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar Amurka
Hukumar ICPC Ta Gayyaci Dangote Labarai
Karo Na Biyu Cikin Kwanaki 29 An Samu Gobara A Kasuwar Katako Labarai
Kasashen Daular Larabawa Tare Da Saudiya Da Jordan Sunyi Allah Wadai Da kasar Israel Afrika
Gwamnatin Tarayya: Bikin Al’adun Argungu Ya Karbu A Idon Duniya Labarai
Bayan Ya Ziyarci Kwankwaso Gawuna Zai Karbi Katin ADC Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Dottin Shara Ya Damu Jama’ar Havana Kasar Cuba Labarai
  • Senegal Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirka Afcon 2025. Wasanni
  • Makiyaya Sun Shiga Matsala Sakamakon Fari A Kasar Kenya Afrika
  • An Bukaci Matasa Su Taka Gagarumar Rawa Wajen Gina Zaman Lafiya A Arewa Maso Gabas Afrika
  • Ministan Harkokin Wajen Rasha Dana Iran Sun Tattauna Don Kawo Karshen Yaki A Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • NEDC Ta Fara Shirin Kera Sanitary Pads A Gombe Domin Samar Da Sana’o’i Afrika
  • Adamu: “Yakar Cin Hanci Daga Tushe Itace Mafita Daya Tilo” Labarai
  • Shugaba Trump Yayi Barazanar Tura Sojoji Ga Masu Zanga Zanga Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.