Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

CNG Ta Farfado Da Jarin Masu Adaidaita Sahu A Kaduna
Published: May 5, 2026 at 3:49 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

A halin yanzu, direbobin baburan adaidaita sahu (keke Napep) a birnin Kaduna sun fara numfasawa biyo bayan rungumar amfani da iskar gas (CNG) wanda ya rage musu radadin tsadar man fetur tare da dawo musu da ribar da suka dade suna nema suka rasa.

Binciken da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya gudanar ya nuna cewa, masu baburan da yawa na tururuwar komawa amfani da gas din, musamman bayan da farashin fetur ya yi tashin gwauron zabi sakamakon janye tallafi a shekarar 2023. Wannan sauyi ya sa da dama daga cikin wadanda suka ajiye sana’ar saboda faduwa, suka koma bakin aiki.

Musa Abdullahi, mai shekaru 38 da ke sana’ar a yankin Tudun Wada, ya bayyana cewa sauya wa zuwa gas ya rage masa asarar kudi.

“A baya, ina kashe kusan N15,000 kullum wajen siyan fetur, har ma wani lokacin idan na koma gida bani da sauran komai. Amma yanzu da iskar gas, abin da nake kashewa bai wuce N2,000 zuwa N3,000 ba,” in ji shi.

Haka shi ma Bala Garba, wanda ke bin hanyar Kawo, ya shaida wa NAN cewa a mako guda yana kashe N18,000 ne kawai a kan gas, sabanin N70,000 da yake babbakawa a baya.

“Dā ma idan na cire kudin mai da na gyara, N20,000 kawai nake tashi da ita a mako. Amma yanzu ina samun tsakanin N45,000 zuwa N50,000.”

Sani Lawal mai shekaru 32, ya ce lissafinsa na wata-wata ya canja. Yayin da dā yake kashe sama da N200,000 a wata wajen man fetur, yanzu da N75,000 kacal yake gudanar da harkokinsa, wanda hakan ke ba shi damar kai wa iyalinsa sama da N100,000 a karshen wata.

Wannan al’amari bai tsaya ga direbobin kadai ba, har ma da fasinjoji. Malama Amina Sule ta bayyana cewa wasu direbobin sun fara rage kudin mota.

“Hanyar da nake biyan N300 dā, yanzu ana dauka ta a kan N200 ko N250. Ko da yake ragi ne kadan, amma ya taimaka mana kwarai.”

Duk da wannan garabasa, masu ruwa da tsaki da kwararru a fannin sufuri sun nuna cewa akwai sauran rina a kaba. Babban abin damuwar masu adaidaita sahun shi ne karancin wuraren sayar da iskar gas din (CNG stations) da kuma tsadar sayen sabbin baburan masu amfani da gas.

Sai dai masana muhalli sun kara da cewa, amfani da iskar gas din ba riba kadai ba ne, yana kuma taimakawa wajen rage gurbatar iska a birane tunda gas din ba ya fitar da hayaki mai guba kamar fetur.

A karshe, Ibrahim Sadiq mai shekaru 27, wanda ya kusa barin sana’ar a shekarar 2025 saboda fatara, ya ce yanzu ya dawo sabon mutum. A cewarsa, idan aka dore a haka, za su iya dogaro da kansu yadda ya kamata.

Afrika, Labarai, Najeriya, Sana'o'i

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Majalisar Wakilai 17 Sun Fice Daga ADC
Next Post: Shugaba Tinubu Ya Taya Murtala Garo Murnar Zama Mataimakin Gwamnan Kano

Karin Labarai Masu Alaka

Rundunar Sojin Amurka Zasu Kaiwa Iran Hari Amurka
Amurka Tace Zata Gama Yakin Iran Cikin Makonni Afrika
Kimanin Ganga Miliyan 40 Na Danyen Albarkatun Mai Yayi Kwantai A Kasashen Afirka Ta Yamma Afrika
Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Kashe-kashen Jos Da Kaduna Afrika
Ukraine Zata Sayi Iskar Gas Daga Mozambique Afrika
Ganduje: Mun Janye Shirin Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jaura Ta Bayyana A Wasu Jihohin Amurka Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Ta Taya Super Eagles Murnar Lashe Tagulla A Gasar AFCON Wasanni
  • Kasashen Yankin Gulf Sun Bukaci Amurka Takawo Karshen Iran Afrika
  • Fadar Shugaban Ƙasan Najeriya Ta Musanta Wani Labarin ƙarya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Abba Kabir: Zamu Samar da Jirage Marasa Matuka A Kano Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wani Alkali A Amurka Ya Kalubalanci Gwamnatin Kasar Afrika
  • An Gabatar Da Sabbin Kudurorin Kare Muhalli Da Gandun Daji A Gombe Afrika
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028 Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.