Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Ana Kokarin Kawo Karshen Matsalar Kashe Matafiya A Filato
Published: May 8, 2026 at 12:52 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: May 8, 2026

Mummunan lamari na kisan mutane da lalata dukiyoyi a jihar Filato ya kasance da matukar damuwa ga al’ummar jihar dake hankoron samun mafita.

Rahoton da wani komiti da gwamnatin jihar Filato ta kafa a shekara ta dubu biyu da ishirin da biyar, karkashin shugabancin Janar Nicholas Rogers ya bayyana cewa daga shekara ta dubu biyu da daya zuwa shekara ta dubu biyu da ishirin da biyar, mutane dubu goma sha daya da dari bakwai da arba’in da tara ne suka rasa ransu, dalilin rikice-rikicen da suka shafi neman wawure filin zama, da na noma da kiwo, ayyukan ‘yan bindiga da bata gari, rikice-rikicen da ake dangantawa da addini da kabilanci da sauransu.

Rahoton yace lamarin ya shafi yankuna dari hudu da ishirin a kananan hukumomi goma sha uku na jihar.

Tun bayan mika rahoton wa gwamnatin jihar Filato, al’ummar jihar, musamman wadanda ke karkara, sun ci gaba da samun kansu cikin wannan mummunan yanayi ba tare da sassauci ba.

A baya-bayan nan, wani lamari dake nema zama ruwan dare a wassu sassan jihar shine yadda matasa ke tare hanya, bayan kaiwa hari a kauye, cikin fushi su kashe ko jikkata matafiya da basu san hawa da sauka ba.

Mai fashin baki kan lamura, musamman a kafar sada zumunta, Steve Davou Damar yace babu addini ko dabi’a da ta goyi bayan kisan wanda bashi da laifi.

Shima shugaban rikon kwarya na gamayyan kungiyoyin matasa a Najeriya, Barista Buhari Ibrahim Shehu yace rashin sanin doka a bangaren matasa na daga dalilan da yasa batun tare hanya a kashe mutane ke ci gaba da aukuwa.

A bangare guda kuwa gwamnatin jihar Filato ta sha alwashin daukan mataki kan duk wanda ya tare hanya da sunan ramako.

Sakataren gwamnatin jihar Filato, Samuel Jatau yace wannan salo da al’ummar Filato ke yi na tare matafiya a kan hanyar gwamnati ba daidai bana, kuma gwamnatin zata dauki mataki.

Duk da shike wannan ba shine karo na farko da gwamnatin ke ikirarin daukan mataki ba, domin a kwanakin baya an jiyo gwamnan jihar Caleb Mutfwang na ikirarin kama duk wani basarake da matasan yankinsa suka tare hanya, to sai dai ko gwamnatin ta kama wani ko a’a, salon tare hanya da keyi a wassu sassan jihar na neman zama nomal, bi ma’ana, lamari na yau da kullum.

Daga Jos Wakiliyar GTA Hausa Amurka Ke Magana Zainab Babaji tana dauke da cikekken rahoton

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/05/AUD-20260508-WA0035.mp3
Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shugaba Tinubu Ya Shiga Takara Wa’adi Na Biyu
Next Post: Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Dawo Da Kudaden Ma’aikata

Karin Labarai Masu Alaka

Ana Tuhumar Dan Shugaba Robert Magabe Da Kisan Kai Afrika
Sojojin Isra’ila Sun Kashe Babban Kwamandan Kungiyar Hezbollah Afrika
Malaman Tsangaya A Gombe Sun Goyi Bayan Inuwa Yahaya Da Jamilu Gwamna Afrika
Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
Kasar Congo Ta Dau Alwashin Bin Tsari Wajen Rarraba Ma’adanai Afrika
China Ta Yi Kira Da Kasashen Gabas Ta Tsakiya Su Hada Kai Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnan Gombe Ya kori Wasu Hadimansa Bisa Cin Zarafin Kansila Najeriya
  • Iran Ta Karyata Tattaunawa Da Washington Afrika
  • Najeriya Na ƙoƙarin Shiga Gasar Cin Kofin Duniya 2026 Ta Barauniyar Hanya Wasanni
  • Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
  • Kyaftin Na Super Eagles Ya Yi Ritaya. Wasanni
  • Wani Bincike Ya Nuna Cewar Da Wuya Iran Ta Bude Mashigin Hormuz Afrika
  • Tinubu Na Kokarin Rage Tsadar Sufuri Ta Hanyar Shirin CNG Afrika
  • Trump Da Bin Salman Da Wasu Kasashe Za Su Sa Hannu A Rikicin Sudan Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.