Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Najeriya Da Amurka Sun Karfafa Alakar Tsaro
Published: May 9, 2026 at 12:56 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kasashen Najeriya da Amurka sun kulla yarjejeniyar kara zurfafa hadin gwiwa a fannin tsaro, yaki da ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin Yammacin Afirka.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Taimakawa Shugaban Kasa kan Yada Labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Asabar, 9 ga watan Mayun 2026.

Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, ya kai ziyarar aiki ta kwanaki uku a Amurka, inda ya gana da manyan kusoshin gwamnatin kasar. A yayin ziyarar, Ribadu ya isar da sakon Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jajircewa wajen dorewar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ribadu ya gana da Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio da Sauran manyan jami’an diflomasiyya da na tsaro na kasar Amurka.

Babban makasudin wannan ganawa shi ne duba yadda za a inganta raba bayanan sirri da kuma karfafa ayyukan soji na hadin gwiwa. NSA Ribadu ya jaddada muhimmancin taimakon juna don magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin Sahel, musamman Ayukan ta’addanci da tsagera, Safarar miyagun kwayoyi da makamai da Laifukan da ake aikatawa ta hanyar yanar gizo.

Hukumomin Amurka sun jinjina wa Najeriya a matsayinta na jagora a yankin Afirka, musamman wajen jagorantar yaki da ta’addanci a tafkin Chadi.

A nata bangaren, Najeriya ta bayyana cewa tana amfani da dabarun karfin soja da kuma tattaunawa da inganta rayuwar jama’a don magance tushen matsalar rashin tsaro.

“Najeriya tana godiya ga Amurka bisa taimakon da take bayarwa a bangaren horar da jami’ai, ba da bayanan sirri, da kuma tallafin jinkai.” — Ribadu

A karshen taron, bangarorin biyu sun amince su ci gaba da tuntubar juna akai-akai ta hanyar hadin gwiwa na musamman don tabbatar da cewa dukkan yarjejeniyoyin da aka kulla sun fara aiki yadda ya kamata.

Afrika, Amurka, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gombe Ta Ƙaddamar da Allurar Rigakafin HIV Ta LEN PrEP
Next Post: Dakaru Sun Hallaka ’Yan Ta’adda Masu Yawa – DHQ

Karin Labarai Masu Alaka

Anyi Rashin ‘Yan Jarida 6 A Jihar Gombe Sakamakon Hatsarin Mota Labarai
Tinubu: Mun Ware Biliyan 42 Don Inganta Lafiyar ‘Yan-Kasa Labarai
Amurka Zatayi Amfani Da Sansanonin Birtaniya Amurka
Kotun Uganda Tayi Watsi Da Karar Hukumomin Kasar Afrika
Gwamnatin Tarayya: Bikin Al’adun Argungu Ya Karbu A Idon Duniya Labarai
Akwai Alamar Shawarwari Tsakanin Amurka Da Turai Zai Kawo Karshen Yakin Rasha Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sojojin Amurka Sun Kutsa Cikin Kasar Iran Labarai
  • Zulum Ya Tallafa Wa Mambobin NYSC Da Naira Miliyan 8.2 A Borno Afrika
  • An Damke Matasa Masu Gurza Kudaden Ketare Na Jabu Afrika
  • Congo Ta Kawo Karshen Cutar Kyandar Birai Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028 Wasanni
  • Anfara Kirga Kuri’a A zaben Kasar Guinea Labarai
  • Anyi Jana’izar Mahaifiyar Nasiru El Rufai A Abuja Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.