Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

NYSC – Sai An Gabatar Da Takardar NERD Kafin Shiga Bautar Ƙasa
Published: May 19, 2026 at 10:42 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar ‘yan yiwa Ƙasa Hidima ta Najeriya, National Youth Service Corps, ta bayyana cewa daga yanzu za ta riƙa tura masu yi wa ƙasa hidima ne kawai idan sun gabatar da takardar shaidar tantancewa daga Nigeria Education Repository and Databank.

Babban Daraktan hukumar, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ne ya sanar da hakan yayin taron shirin tura masu yi wa ƙasa hidima na rukuni na “B” na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.

Ya ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Najeriya na daƙile amfani da jabun takardun kammala karatu tare da tabbatar da cewa sahihan waɗanda suka kammala karatu ne kawai ake bai wa damar gudanar da bautar ƙasa.

Janar Nafiu ya yi kira ga jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi masu fitar da ɗalibai zuwa bautar ƙasa da su ƙara wayar da kan ɗalibansu kan muhimmancin bin sabon tsarin tare da tabbatar da cikakken aiwatar da shi.

A cewarsa, aikin tantancewa da tura masu yi wa ƙasa hidima ba nauyin NYSC kaɗai ba ne, yana mai jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, cibiyoyin ilimi, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da gaskiya, inganci da amincin tsarin bautar ƙasa.

Tun da farko, Daraktar Sashen Tura Masu Yi wa Ƙasa Hidima ta NYSC, Misis Rachel Ideawor, ta bayyana taron a matsayin wata muhimmiyar dama ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumar da cibiyoyin ilimi domin inganta tsarin tura masu yi wa ƙasa hidima a faɗin ƙasar.

Ta kuma buƙaci jami’an kula da harkokin ɗalibai su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da riƙon amana tare da tabbatar da cewa bayanan da ake aikawa sun dace da ainihin bayanan masu shirin bautar ƙasa.

Taron ya samu halartar wakilai daga Joint Admissions and Matriculation Board, National Universities Commission, National Board for Technical Education, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da sauran hukumomin da ke da ruwa da tsaki a harkar ilimi da bautar ƙasa a Najeriya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Shirye-Shirye

Post navigation

Previous Post: Sanata Goje: Sakamakon Zaben Daga Abuja Zai Fito
Next Post: Zargin Tauye Ka’idojin Zabe: Malam Pantami Ya Janye Daga Takara

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Tinubu Ta Karyata Kafa Kamfanin Gwal A Legas Labarai
‘Yan Kasashen Afirka Da Dama Suna Fafatawa Da Rasha A Yaki Da Ukraine Afrika
Tarkacen Makamai Masu Linzami Sun Lalata Gidaje Da Wuraren Kasuwancin Palasdinawa Afrika
Amurka Zata Fice Daga Iran Cikin Gaggawa Afrika
Kungiyar ECOWAS Ta Koka Game Da Yawan Juyin Mulki A Kasashen Afirka Afrika
’Yar Kasuwa Ta Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Hari Da Saurayinta Ya Kai Mata Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Belarus Zata Taffawa Jamhuriyar Nijar Afrika
  • Iran Zata Kai Hari Tashar Makamashin Ruwa A Gulf Afrika
  • Trump: Isra’ila Ta Daina Kai Hari Ga Duk Cibiyar Iskar Gas Afrika
  • Najeriya, Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 80, Sun Ceto 34 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ferfesa Pantami Yayi Watsi Da Amincewa Da Jamilu Isiyaku Gwamna Afrika
  • Zelensky Na Ukraine Zai Gana Da Takwaransa Na Faransa A Yau Labarai
  • Chelsea Tayi Kaca-Kaca Da Barcelona A Gasar UCL Wasanni
  • Rundunar Sojin Iran Tace Harin Amurka Ya Kashe Musu Sama Da Mutane Dari Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.