Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Zargin Tauye Ka’idojin Zabe: Malam Pantami Ya Janye Daga Takara
Published: May 19, 2026 at 7:31 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani na Najeriya, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na kujerar gwamnan jihar Gombe karkashin jam’iyyar All Progressives Congress APC.

A cikin wata sanarwa da Barista Ibrahim M. Attahir ya fitar a madadin kungiyar Pantamiyya Movement a ranar 19 ga Mayun 2026, Pantami ya ce ya dauki matakin ne domin nuna rashin amincewa da abin da ya kira karya dokar zabe ta 2026 da kuma rashin samar da ingantaccen tsarin gudanar da zaben fidda gwani.

Sanarwar ta ce Pantami ya shiga takarar ne bayan kiraye-kirayen da ya samu daga matasa, mata, shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki a jihar, inda ya bi dukkan sharudda da ka’idojin jam’iyyar APC.

Ta kara da cewa Pantami ne kadai cikin masu neman takarar gwamna a APC da ya tura wakili zuwa taron yarjejeniyar zaman lafiya da Nigeria Police Force reshen jihar Gombe ya shirya ranar 14 ga Mayun 2026, kuma wakilinsa ne kadai ya sanya hannu kan yarjejeniyar.

Sai dai sanarwar ta zargi shugabannin jam’iyyar da kin bayar da muhimman bayanai dangane da yadda za a gudanar da zaben fidda gwani, ciki har da wuraren kada kuri’a, tsarin tantance wakilai da masu sa ido, da cibiyoyin tattara sakamako.

Pantami ya kuma yi zargin cewa zabukan fidda gwani na ‘yan majalisar tarayya da APC ta gudanar a ranakun 16 da 18 ga Mayun 2026 ba su bi ka’idojin dimokuradiyya ba, yana mai cewa an ware ‘ya’yan jam’iyyar na kasa musamman matasa da mata daga tsarin zaben.

Sanarwar ta ce duk da umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci, ba a aiwatar da wadannan umarni yadda ya kamata ba a jihar Gombe.

Pantami ya gode wa matasa da suka hada kudade domin sayen fom dinsa na nuna sha’awa da takara, inda gudummawar ta kai daga naira dubu biyar zuwa miliyan hudu, tare da bayyana cewa an gudanar da komai a fili.

Ya kuma yaba wa magoya bayansa, musamman matasa da mata, da masu ruwa da tsaki daga mazabu, kananan hukumomi da daukacin jihar Gombe bisa goyon baya da hadin kai.

A karshe, Pantami ya bukaci mabiyansa da su kasance masu bin doka da oda tare da tabbatar da zaman lafiya a jihar, yana mai cewa kungiyar Pantamiyya za ta sanar da matakinta na gaba nan gaba kadan.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: NYSC – Sai An Gabatar Da Takardar NERD Kafin Shiga Bautar Ƙasa
Next Post: Sanata Sa’idu Alkali Ya Kaurace Wa Zaben Fidda Gwani

Karin Labarai Masu Alaka

An Farmaki ‘Yan Bindiga Da Dama A Jihar Zamfara Labarai
Hukumar Zabe A Kasar Honduras Ta Sanar Da Nasry Asfura A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Ƙasa Afrika
Nada Jakadu Da Tinubu Yayi Sako Ne Ga ‘Yan-Arewa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kakakin Majalisar Kasar Amurka Yana Tsaka Mai Wuya Game Da Kasafin Kudi Amurka
An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Iran Zata Kai Hari Tashar Makamashin Ruwa A Gulf Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jama’a A Yankin Gulf Sun Bukaci Dakatar Da Hare Hare Daga Washington Afrika
  • Ruwan Sama Yayi Ajalin Daruruwan Mutane A Afirka Ta Kudu Afrika
  • NFF Ta Nada Eguavoen Kocin Rikon Kwarya Na Super Falcons Wasanni
  • Shirin Kwace Iyakar Greenland Da Shugaba Trump Yakeyi Yabawa Kasashen Turai Mamaki Amurka
  • Pakistan Da Afghanistan Sun Shiga Kwana Na Biyar Suna Fafatawa Afrika
  • Cutar Kurkunu Ta Kusa Zamowa Tarihi A Duniya Amurka
  • Turkiyya Tana Gudanar Da Binciken Kasar Da Suka Kona Tutar Ta Tsaro
  • Mace Ta Farko Da Zata Shugabanci Jami’ar Northwest Dake Kano Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.