Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi
Published: May 29, 2026 at 9:54 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta samu nasarar shimfiɗa tubalin farfaɗo da tattalin arziki da sake daidaita al’amuran ƙasa bayan shekaru uku da hawansa mulki.

Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar domin cika shekara uku cif na gwamnatin sa a ranar 29 ga watan Mayun 2026.

Shugaban ƙasar ya ce lokacin da ya karɓi mulki a shekarar 2023, Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki, ƙarancin kudaden shiga, matsalar tsaro da kuma tabarbarewar harkokin gwamnati.

Ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakai masu wahala amma masu muhimmanci domin ceto ƙasar daga durƙushewar tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur da kuma gyaran tsarin musayar kuɗaɗen waje.

A cewarsa, Najeriya na kashe kusan naira biliyan 18.4 a kullum wajen tallafin man fetur kafin cire shi, lamarin da ya ce yana hana zuba jari a bangarorin raya ƙasa kamar hanyoyi, lafiya da ilimi.

Tinubu ya amince cewa matakan da gwamnatin ta ɗauka sun jawo tsadar rayuwa da wahalhalu ga jama’a, amma ya jaddada cewa sadaukarwar da ’yan Najeriya suka yi ba ta tafi a banza ba.

“Yanzu Najeriya ta fara samun daidaito kuma tana ci gaba a hankali,” in ji shi.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya kara ƙarfi idan aka kwatanta da shekarar 2023, yana mai cewa kasuwar hannayen jari ta ƙaru daga naira tiriliyan 30 zuwa tiriliyan 160.

Ya kuma ce gwamnatin sa na gudanar da manyan ayyukan hanyoyi sama da kilomita 2,700 a faɗin ƙasar nan, ciki har da titin Lagos-Calabar Coastal Highway, Sokoto-Badagry Super Highway da kuma hanyar Abuja zuwa Kano.

A bangaren mai da gas, Tinubu ya ce gyare-gyaren da gwamnati ta yi sun jawo sabbin jarin biliyoyin daloli tare da bunƙasa matatun mai na cikin gida domin rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

Game da wutar lantarki, shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin magance matsalolin da suka dabaibaye bangaren tsawon shekaru ta hanyar inganta layukan sadar da wuta da kuma zuba jari a makamashi.

A bangaren noma kuwa, ya ce gwamnati ta tallafa wa miliyoyin manoma da iri, taki, injina da hanyoyin samun rance domin bunƙasa samar da abinci da rage tsadar rayuwa.

Tinubu ya kuma bayyana cewa Asusun Lamunin Dalibai na Najeriya ya taimaka wa sama da dalibai miliyan 1.5 da kudade sama da naira biliyan 282 domin ci gaba da karatu.

Haka kuma ya ce gwamnati na ci gaba da gina gidaje masu araha a jihohi daban-daban tare da samar da dubban ayyukan yi ga matasa.

Dangane da tsaro, shugaban ƙasar ya ce jami’an tsaro sun ƙara kaimi wajen yaki da ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka, yana mai cewa an fara samun saukin matsalar tsaro a wasu yankuna.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da haɗa kai tare da nuna haƙuri da fatan alheri ga ƙasa.

“Dole mu fifita haɗin kai a kan rarrabuwar kawuna, da fata mai kyau a kan yanke ƙauna,” in ji shugaban ƙasar.

Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin rage tsadar rayuwa tare da samar da karin damammakin ayyukan yi da bunƙasa kasuwanci.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Atiku Ya Bukaci Hadin Kan ‘Yan Adawa Domin Kawo Sauyi A Najeriya
Next Post: Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa

Karin Labarai Masu Alaka

Sanata Sa’idu Alkali Ya Kaurace Wa Zaben Fidda Gwani Afrika
Dusar Kankara Ta Hana Jirage Tashi A Birnin Paris Labarai
Gwamnatin Jihar Filato Ta Sauke Hakimin Mushere Afrika
Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Harin Jos Afrika
Usman Maiyama Ne Gwarzon Kamun Kifin Argungu Bana Labarai
Hukumar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Jama’ar Jos Ta Arewa Su Rika Bin Doka Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ƙungiyar Mata Sunyi Kira Ga Jam’iyar P R P Da Ta Dauki Baheejja A Matsayin Mataimakiyar Gwamnan A Bauchi 2027 Labarai
  • Hukumar Hakar Ma’adanai A Kasar Zambiya Ta Dakatar Da Ayyukanta Kimiya
  • EFCC Ta Tsare Tsohon Minista Abubakar Malami Tsaro
  • Shugaba Bola Tinubu Ya Tafi Turai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Anfara Gangamin Kafa Dokoki Masu Tsanani Ga ‘Yan Luwadi A Senegal Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • An Dakatar Da Daniel Bisa Zargin Fyade Wasanni
  • Shugabannin Kasashen Sahel Sunyi Taro a Mali Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.