Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Masu Luwadi Na Fuskantar Tara Da Daurin Shekaru 20 A Nijar
Published: June 12, 2026 at 10:27 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kafa sabuwar doka da ta haramta luwadi, madigo da kuma duk wata alaƙa ta aure tsakanin masu jinsi guda, tare da tanadar hukunci mai tsauri ga duk wanda aka samu da laifin karya dokar.

Dokar, wadda shugaban ƙasar, Janar Abdourahamane Tiani, ya sanya wa hannu, ta tanadi tarar kuɗi har zuwa CFA miliyan 100 da kuma ɗaurin shekaru aƙalla 20 a gidan yari ga duk wanda aka samu da aikata irin waɗannan laifuka.

Matakin ya zo ne a yayin da ake samun rahotannin cewa hukumomin ƙasar na gudanar da bincike kan wasu mutane da dama da ake zargi da hannu a ayyukan da dokar ta haramta. Rahotannin sun kuma nuna cewa wasu daga cikin waɗanda ake binciken manyan ma’aikatan gwamnati ne.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin Nijar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance da ke bayyana cikakken bayani kan binciken da ake yi ko kuma adadin mutanen da abin ya shafa ba.

Masu lura da al’amuran siyasa da zamantakewa na ganin wannan mataki wani muhimmin sauyi ne a tsarin dokokin ƙasar, wanda ka iya jawo martani daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da sauran masu ruwa da tsaki a cikin gida da wajen Nijar.

A halin yanzu, gwamnati ba ta bayyana cikakkun matakan aiwatar da sabuwar dokar ba, yayin da ake ci gaba da sa ido kan yadda lamarin zai kasance a nan gaba.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i

Post navigation

Previous Post: Sakon Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu A Ranar Dimokraɗiyya Ta 2026
Next Post: Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Ya Rasu A Abuja Bayan Doguwar Jinya

Karin Labarai Masu Alaka

Harin Makami Mai Linzami Da Rasha Ta Kai Yayi Barna Sosai A Ukraine Afrika
Yanayin Yunwa Yana Kara Ta’azarra A Somaliya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Wani Jami’in Iran Yace Amurka Taso Kanta A Tattaunawar Tsagaita Wuta Amurka
Farashin Danyen Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Afrika
Gombe Ta Ƙarfafa Ilimin Almajirai Da Tsangaya Don Rage Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta Afrika
Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dawo Da Dokar Zirga Zirgar Babura A Jihar Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Farashin Gangar Mai Yayi Gagarumar Fadi A Kasashen Duniya Labarai
  • Rundunar ‘Yan Sanda Sun Ceto Wani Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
  • Kasar Tanzaniya Zata Gina Babban Tashar Iskar Gas Labarai
  • Yakin Gabas Ta Tsakiya Ya Kawo Cikas Ga Cinikin Nama A Kenya Afrika
  • Madrid, Arsenal Da Chelsea Sun Fara Zaurancen Dan-Wasa Kenan Yildiz Wasanni
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • Sanata Goje Yayi Watsi Da Fidda ‘Yan Takarar APC A Gombe Afrika
  • RSF Ta Nemi A Gaggauta Gano Dan Jarida Moussa Kaka Da Ya Bace A Yamai Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.