Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ahmed Gara Ya Kaddamar da Kofin Sarkin Gombe, Ya Jaddada Bunƙasa Matasa Afrika
  • Anyi Jana’izar Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Afrika
  • Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Ya Rasu A Abuja Bayan Doguwar Jinya Afrika
  • Masu Luwadi Na Fuskantar Tara Da Daurin Shekaru 20 A Nijar Afrika
  • Sakon Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu A Ranar Dimokraɗiyya Ta 2026 Afrika

Janar Rabe Abubakar Ya Mutu A Tsare A Hannun Masu Garkuwa Da Mutane
Published: June 13, 2026 at 7:57 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: June 13, 2026

Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda ya rasu yayin da yake tsare a hannun ‘yan bindiga bayan sace shi.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Gida na jihar, Dakta Nasiru Mu’azu, ya fitar, gwamnatin ta bayyana alhininta kan wannan lamari, tana mai cewa rasuwar marigayin babban rashi ne ga iyalansa, Jihar Katsina da kuma Najeriya baki ɗaya.

Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka haɗa da ciwon sukari da hawan jini yayin da yake tsare. Ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar tare da hukumomin tsaro sun yi ƙoƙari matuƙa domin ganin an kuɓutar da shi cikin koshin lafiya kafin rasuwarsa.

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da daukacin al’ummar ƙasar nan, inda ya bayyana lamarin a matsayin wani lokaci na baƙin ciki da ke nuna muhimmancin ƙara haɗa kai wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro da ayyukan ‘yan bindiga.

Gwamnan ya kuma jaddada kudirin gwamnatin jihar na ci gaba da aiki tare da Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro domin tabbatar da an hukunta masu hannu a wannan aika-aika tare da ƙarfafa matakan samar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.

Gwamnatin Katsina ta kuma tabbatar wa al’umma cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen yaƙi da ‘yan bindiga da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar ya kasance ɗaya daga cikin manyan hafsoshin sojin Najeriya da suka yi wa ƙasa hidima tsawon shekaru, kuma za a ci gaba da tunawa da gudunmawar da ya bayar wajen kare martabar ƙasar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Anyi Jana’izar Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo
Next Post: Ahmed Gara Ya Kaddamar da Kofin Sarkin Gombe, Ya Jaddada Bunƙasa Matasa

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar China Ta Sauka Daga Ragamar Bada Bashi Labarai
An Gano Kwale-Kwalen Fir’auna A Birnin Masar Afrika
Kasar Malawi Ta Kaddamar Da Rigakafin Shan Inna Kiwon Lafiya
Kasar Saudiya Ta Sanar Da Ganin Watan Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Asusun IMF Zasu Ziyarci Kasar Gabon Afrika
Gwamnatin Kano Ta Rufe Gidajen Bukukuwa Da Shakatawa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ahmed Gara Ya Kaddamar da Kofin Sarkin Gombe, Ya Jaddada Bunƙasa Matasa
  • Janar Rabe Abubakar Ya Mutu A Tsare A Hannun Masu Garkuwa Da Mutane
  • Anyi Jana’izar Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo
  • Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Ya Rasu A Abuja Bayan Doguwar Jinya
  • Masu Luwadi Na Fuskantar Tara Da Daurin Shekaru 20 A Nijar

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Za’ayi Auren Zawarawa Dubu Uku A Kano Afrika
  • Hamma Saleh Ya Yi Fatali da Bai Wa Pantami Takarar Gwamna a PDP Afrika
  • Wasu Kasashen Turai Zasu Daina Tura Sojinsu Wata Cibiyar Sojojin Amurka Amurka
  • Sanata Barau Ya Raba Motoci Da Babura Ga Al’ummar Kano Ta Arewa Afrika
  • INEC Mayar Da Lokacin Zaɓen 2027 Kafin Azumi Najeriya
  • Yan Fashi Sun Shiga Gidan Alex Iwobi A Ingila Wasanni
  • Kungiyar ISIS Ta Kashe Sojojin Amurka Biyu Amurka
  • Mutane Biyu Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Da Ya Rutsa Da Antothy Joshua Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.