Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Shugaba Tinubu Ya Yabawa Dakarun Tsaro Bisa Ceto Matar Marigayi Janar Rabe
Published: June 16, 2026 at 2:07 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa rundunar sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa nasarar da suka samu a wani samame da aka gudanar a Jihar Kogi, wanda ya kai ga kashe fitaccen shugaban ’yan bindiga, Ibrahim Bastuji.

A cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Litinin, Tinubu ya bayyana wannan nasara a matsayin wani babban koma baya ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka da suka daɗe suna addabar al’ummomi a Kogi da jihohin da ke maƙwabtaka da ita.

Shugaban ƙasar ya ce Bastuji ya yi kaurin suna wajen jagorantar hare-hare, sace-sacen mutane da sauran ayyukan ta’addanci da suka jefa mazauna yankunan cikin wahala da fargaba.

Ya ce kashe shi zai taimaka wajen dawo da kwanciyar hankali tare da ƙarfafa gwiwar al’umma kan cewa hukumomin tsaro na ci gaba da samun nasara a yaƙin da suke yi da masu aikata laifuka.

“Ina taya jaruman dakarunmu murnar wannan gagarumar nasara. Najeriya ba za ta miƙa ko da inci ɗaya na ƙasarta ga masu laifi ba. Duk wanda ya zaɓi hanyar tada hankali da zubar da jinin bayin Allah, ba zai samu mafaka ba. Wannan nasara ta nuna ƙudurin jami’an tsaronmu na tabbatar da tsaro a ko’ina cikin ƙasar nan,” in ji Tinubu.

Hakazalika, shugaban ƙasar ya yabawa jami’an tsaron kan nasarar da suka samu wajen ceto Hajiya Amina Rabe Abubakar, matar marigayi tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Janar Rabe Abubakar mai ritaya.

Tinubu ya ce ceto ta cikin koshin lafiya ya nuna ƙwarewa, jajircewa da haɗin gwiwar da jami’an tsaro ke nunawa wajen yaƙi da masu aikata miyagun laifuka.

“Dawowar Hajiya Amina gida cikin aminci abin farin ciki ne ga iyalanta da kuma daukacin ’yan Najeriya. Ina yaba wa jami’an da suka shirya tare da aiwatar da wannan aiki cikin nasara. Hakika muna bin dakarunmu bashin godiya saboda sadaukarwar da suke yi kullum domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” in ji shugaban ƙasar.

Tinubu ya kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da samar wa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro kayan aiki, horo da tallafin da suke bukata domin kawo ƙarshen matsalolin ’yan bindiga, satar mutane da sauran nau’o’in aikata laifuka a ƙasar.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen yaƙi da rashin tsaro.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sabuwar Shekarar Musulunci 1448: Kiristoci Sun Yi Murna, Sunyi Kiran Samar Da Hutu Ga Shekarar Musulunci
Next Post: Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Lakurawa

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Da Isra’ila Sunkai Hari Kan Iran Amurka
Iran Ta Karyata Tattaunawa Da Washington Afrika
Shugaban Najeriya Tinubu Ya Amince Na Tura Jakadu Labarai
Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki Labarai
Bankin Duniya Zaibawa Kasar Mozambique Lamunin Dala Bilyan Shida Labarai
Yaki Ta Sararin Samaniya Ya Cigaba Tsakanin Amurka, Isra’ila Da Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Baba Buhari Yayi Zargin Ansaka Masa Na’urar Tsaro Labarai
  • Zargin Tauye Ka’idojin Zabe: Malam Pantami Ya Janye Daga Takara Afrika
  • Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sarakunan Gombe Da Zazzau Sun Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Su Rungumi Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Don Neman Zaman Lafiya Labarai
  • Nasarawa Ce Zakara A Wasan Kwallon Kafa Ta Kurame 2025 Wasanni
  • Muhawara Mai Zafi Tsakanin APC da ADC Shirye-Shirye
  • Gombe Ta Yi Kira Ga Jami’o’i Su Tallafa Wa Gwamnati Ta Hanyar Bincike Da Ƙirƙire-ƙirƙire Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.