Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda (DIG) mai kula da shiyar Arewa Maso Gabas, Zakariyya Fera, da Ibrahim Baba Zango sun buƙaci masu ruwa da tsaki da su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin daƙile ayyukan masu aikata laifuka da magance matsalolin tsaro a yankin.
DIG Fera da Baba Zango sun bayyana hakan ne a yayin taron tuntuba da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe.

A jawabinsa na maraba, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya ce rundunar na ci gaba da ba da fifiko ga aikin ’yan sanda na kusanci da al’umma da kuma inganta tsaro ta hanyar haɗin gwiwa da jama’a.
Da yake jawabi a taron, DIG Fera ya ce manufar ziyararsa ita ce neman haɗin kai da goyon bayan masu ruwa da tsaki wajen yaƙi da masu aikata laifuka. Ya jaddada cewa rundunar ’yan sanda ba za ta iya cimma nasara a aikinta ba tare da sahihan bayanan sirri, haɗin kan al’umma da musayar ra’ayoyi masu amfani daga jama’a.
Ya bayyana cewa tsarin gudanar da aikin ’yan sanda ya kan bambanta daga jiha zuwa jiha, gwargwadon irin ƙalubalen tsaron da ake fuskanta a kowace jiha. Ya kuma ce Sufeto Janar na ’Yan Sanda na ci gaba da ƙarfafa tsarin aikin tsaro da ya ginu kan haɗin kai da jama’a.

DIG ɗin ya yi gargaɗi kan take haƙƙin ɗan Adam, rashin ɗa’a daga wasu jami’an tsaro, rikice-rikicen tsakanin al’umma da sauran ayyukan da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya. Ya tabbatar da cewa rundunar tana da manufar rashin lamuntar duk wani nau’i na cin zarafi, rashin ɗa’a ko karya doka daga jami’anta.
Ya ƙara da cewa Sufeto Janar na ’Yan Sanda na neman cikakken goyon bayan jama’a domin cimma manufofin rundunar, musamman wajen hana aikata laifuka da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
A jawabinsa Sakataren Gwamnatin jihar Gombe, Wanda yasamu wakilincin Alhaji Salihu Adamu Sambo, Babban Sakatare a Ofishin Sakataren Gwamnatin jihar ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya ce babu wani ci gaba mai ma’ana da za a samu ba tare da zaman lafiya da tsaro ba, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bai wa hukumomin tsaro cikakken goyon baya.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta kafa Gombe State Security, Traffic and Environmental Corps (GOSTEC) domin haɗa kai da sauran hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Hakazalika, ya yi kira ga al’umma da su taka muhimmiyar rawa wajen magance tushen matsalolin rashin tsaro ta hanyar haɗin kai, sa ido da kuma bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro.
A nasu jawaban, Sakataren Jama’atu Nasril Islam, Malam Saleh Danburam, Shugaban Kwamitin Hulɗa Tsakanin ’Yan Sanda da Al’umma (PCRC), Kwamared Garba Ubale, da Shugaban Ƙungiyoyin Farar Hula, Ibrahim “3000”, sun yaba da kyakkyawar alaƙa da haɗin gwiwar da ke tsakanin hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a jihar.
Sun kuma yi alƙawarin ci gaba da bai wa jami’an tsaro cikakken haɗin kai da goyon baya, tare da yabawa kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da al’ummar Jihar Gombe, musamman ƙarƙashin jagorancin CP Umar Ahmed Chuso.
Masu jawabin sun yaba da saurin kai ɗauki da rundunar ’yan sandan jihar ke yi a lokutan gaggawa, tare da kira gare ta da ta ci gaba da wannan kyakkyawan aiki domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.


