Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnatin Soji A Nijar Ta Hana Fitar Da Albarkatun Kasa
Published: November 29, 2025 at 8:41 PM | By: Yusuf Aliyu Harande | Updated: November 29, 2025

Kamfanin Orano ya sanar cewa hukumomn Nijar sun fara aiyukan fitar da ton ton na Uranium daga garin Arlit zuwa waje ba tare da sanar da shi ba. Matakin da kamfanin na Faransa ya ce ya saba wa umurnin kotun bankin duniya, wace ta bukaci bangarorin su jira ta kammala shari’ar da ke gabanta.
Kawo yanzu ba wata sanarwa daga bangaren gwamnatin Nijar  sai dai kwararru kan sha’anin ma’adanai sun fara bayyana matsayinsu.
A kalla ton 1300 na Uranium ne ke jibge a kamfanin SOMAIR da ke Arlit na arewacin Nijar bayan da gwamnatin kasar ta dakatar da fitarwa zuwa waje a washegarin juyin mulkin Yulin 2023, saboda abin da suka kira rashin haske daga kamfanin Orano da ke harkar Uranium shekaru sama da 50.
Dangantaka ta ci gaba da tsami a tsakanin bangarorin biyu abin da ya sa Orano shigar da kara a kotun CIRDI domin ta shiga tsakani. A yayin da ake jiran matsayin kotun kamfanin na Faransa ya sanar cewa motoci dauke da lodin Uranium sun fara dagawa daga Arlit zuwa Agadez a yunkurin Isa gabar teku. Kwararre kan sha’anin albarkatun karkashin kasa Mahamadou Tchiroma Aissami na fassara abin a matsayin ci gaban takaddama.
Kamfanin na Orano ya ce fitar da Uranium a wannan lokaci ya saba wa umurnin kotu. sai dai ‘yan Nijar irinsu masani a harakar makamashi injiniya Rabiou Malan Issa na ganin koma mai ake ciki Nijar ce uwar gijiyar albarkatun da ake rikicin kan su.
 Nijar na daga cikin kasashen da suka rattaba hannu kan yarjeniyoyin hakar ma’adanai da hanyoyin sayar da su a kasuwannin duniya, dalili kenan wadanda suka lakanci fannin ke gargadin mahukunta a kan hanyoyin mafita.
 Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen da suka fi kowa yawan Uranium a duniya sai dai alamu na nunin kasar da al’ummarta ba su amfana da arzikin, kamar yadda ya dace abin da ya sa gwamnatin CNSP ta dage da yunkurin sabunta abokan hulda a wannan fanni kuma bayanai na cewa kamfanin ROSATOM na Russia na daga cikin masu fatan ganin an ba su dama.
Afrika

Post navigation

Previous Post: Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Aika Sammaci Dr. Yusuf Baba-Ahmed
Next Post: Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba!

Karin Labarai Masu Alaka

Ambaliyar Ruwa Ya Tilastawa Dubban Jama’a Rasa Muhallensu A Morocco Afrika
‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini Afrika
Harin Makami Mai Linzami Da Rasha Ta Kai Yayi Barna Sosai A Ukraine Afrika
Wani Bincike Ya Nuna Cewar Da Wuya Iran Ta Bude Mashigin Hormuz Afrika
NANPAN Ta Wayar Da Al’umma Kan Amfanin Shayar Da Jarirai Nono Kaɗai Afrika
Shugaban Kasar Faransa Ya Zanta Da Shugaban Kasar Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu Zai Kara Karbo Bashin Dala Miliyan 516 Afrika
  • SERVICOM, ATBUTH Ta Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Damfara Ne Labarai
  • Harin Ukraine Yayi Mummunan Barna A Rasha Afrika
  • Kotun Amurka Ta Soke Harajin Fito Da Shugaba Trump Ya Kakabawa Kayan Kasashen Waje Amurka
  • ADC Ta Sha Damarar Gwabzawa Da APC A Zaben 2027 Shirye-Shirye
  • Kasar Mauritius Zata Rage Amfani Da Makamashi Afrika
  • Ansamu Girgizar Kasa A Kasar Taiwan Labarai
  • ‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Sojoji Da Fararen Hula A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.