Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Tinubu Ya Kawo Ƙarshen Aikin Kwamitin Sayar Da Kaddarorin Gwamnati
Published: July 30, 2026 at 8:21 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da rushe Kwamitin Shugaban Ƙasa mai kula da aiwatar da harkokin sayar da kaddarorin Gwamnatin Tarayya (Presidential Implementation Committee – PIC), tare da ba da umarnin aiwatar da matakin nan take.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, inda ya bayyana cewa daga yanzu dukkan harkokin da suka shafi ayyukan kwamitin za su koma ƙarƙashin kulawar Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi.

Sanarwar ta tuna cewa an kafa kwamitin ne a shekarar 2000, a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, domin kula da sayarwa da bayar da hayar filaye da sauran kaddarorin Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin tsarin Monetisation Policy.

Ta ce bayan nazari mai zurfi, Gwamnatin Tarayya ta gano cewa ayyukan kwamitin sun kauce daga ainihin manufar da aka kafa shi domin aiwatarwa, lamarin da ya janyo ƙararraki masu yawa a kotuna a sassan ƙasar nan.

A sakamakon haka, gwamnatin ta yanke hukuncin cewa babu wata buƙatar ci gaba da wanzuwar kwamitin.

Saboda haka, Shugaba Tinubu ya umarci a rushe kwamitin daga ranar 5 ga Nuwamban 2025, tare da ɗora wa Babban Lauyan Tarayya alhakin kula da dukkan harkokin da suka shafi ayyukan kwamitin.

Haka kuma, Shugaban Ƙasar ya umarci tsohon Sakataren kwamitin, B. S. Dutsin-Ma, da ya dakatar da duk wani aiki ko wakilci da yake yi a madadin kwamitin ko Gwamnatin Tarayya kan duk wani lamari da ya shafi ayyukansa.

Sanarwar ta ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na inganta yadda ake tafiyar da harkokin kadarorin gwamnati cikin tsari, gaskiya da inganci.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya, Shirye-Shirye, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Haɗin Gwiwar GOSERC Da Savannah Zai Ƙarfafa Rarraba Wutar Lantarki A Faɗin Jihar Gombe
Next Post: Gwamnatin Najeriya Ta Jaddada Aniyarta Ta Daƙile Yaɗuwar Makamai Ba Bisa Ƙa’ida Ba

Karin Labarai Masu Alaka

Majalisar Kwararrun Iran Ta Sanar Da Sabon Shugaban Addini Afrika
Sabunta Manhajar Ilimi A Duk Matakai Nasara Ce! Najeriya
NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
Najeriya Zata Kara Mai Da Take Hakowa Afrika
Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11 Afrika
Sanyin Hunturu Yayi Ajalin ‘Yan Cirani A Morocco Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rikicin Gabas Ta Tsakiya Ya Haifar Da Tsadar Man Fetur A Najeriya Afrika
  • Bana Ba Harka Ga ‘Yan-Wasan Kwallon Kafar Najeriya Wasanni
  • Kyautata Dangantaka Tsakanin Jami’an Tsaro Da Al’umma Ce Mafita Najeriya
  • Dan Hamayya Ya Amince Da Faduwa A Zaben Kasar Benin Afrika
  • Rikicin Siyasa A Jihar Rivers Sakamakon Ayyana Fubara A Matsayin Shugaban APC Siyasa
  • Dusar Kankara Ta Hana Jirage Tashi A Birnin Paris Labarai
  • Jana’izar Jagoran Ƙolin Iran Ta Kawo Tsauraran Matakan Tsaro A Tehran Afrika
  • Gwannatin Jihar Kebbi Ta Arawa Maniyyata Kuɗin Aikin Hajji 2026, Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.