Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
Published: August 12, 2026 at 3:34 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su, tare da hallaka ’yan ta’adda 19 a wasu samame da sintiri da aka gudanar a sassan kasar cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

A Zamfara, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 18 da aka yi garkuwa da su a Sabon Gari, karamar hukumar Kaura Namoda, bayan da suka mayar da martani ga kiran neman agaji, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan tserewa.

A Jihar Filato kuma, sojoji sun ceto wani mutum da aka sace daga Duguri a Bauchi, yayin da Operation ENDURING PEACE ta hallaka wani dan ta’adda tare da kwato AK-47 da harsasai biyu.

A Kebbi, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun hallaka ’yan ta’adda 18 yayin da suka kai hari kan jami’an Mobile Police Special Intervention Squad a Makuku, karamar hukumar Sakaba. Sojojin sun kuma lalata babura biyar tare da kwato bindigogi AK-47 guda biyu da aka kera a gida a wani samame a Filato.

A Borno, dakarun Operation HADIN KAI sun ceto mutane biyar da suka tsere daga wani sansanin ’yan ta’adda a yankin tsaunukan Mandara, bayan rikici ya barke tsakanin ’yan ta’addan. A Enugu kuwa, sojoji sun kwato AK-47 guda hudu, magazin bakwai da harsasan 7.62mm guda 133 daga maboyar masu garkuwa da mutane a dajin Umuchingu Ujenike.

A Taraba, dakarun sun kama mutane 19 da ake zargi da aikata laifuka a karamar hukumar Gashaka, tare da kwato babura, injinan famfo, wayoyin hannu da kudade. Rundunar ta ce ayyukan na daga cikin kokarin da take yi na amfani da bayanan sirri, sintiri da samame domin dakile ayyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a sassan Najeriya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
Next Post: CP Chuso Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Gwiwar Hukumomin Tsaro A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar Raya Birane Ta Rushe Gine-Ginen Da Suka Keta Dokokin Tsara Birane A Gombe Labarai
Kurdawa Sun Gargadi ‘Yan Uwansu Game Da Alaka Da Amurka Wajen Yakar Iran Afrika
Sojin Kasar Congo Da ‘Yan Tawaye Sun Kara Shiga Yankin Uvira Labarai
Jirgin Ruwa Ya Kife A Yammacin Kasar Gambiya Labarai
Mutum Mafi Tsufa A Saudiyya Ya Rasu Yana Da Shekaru 142 Labarai
Iran: Za A Gudanar Da Jana’izar Khamenei Bayan Kwanaki Goma Na Muharram Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Abba Kabir: Zamu Samar da Jirage Marasa Matuka A Kano Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Akwai Bukatar APC Tayi Gyare-Gyare Kafun Zabe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Zata Farfado Da Cibiyar Koyon Sana’oi Ta Dangote Afrika
  • Sarkin Gombe Yayin Hawan Tudun Wada Labarai
  • Gwamnan Gombe Ya Ƙara Tallafin N148.76bn Domin Aiwatar da Sabon Tsarin Albashi A Jami’ar Gombe Afrika
  • Afirka Ta Kudu Ta Bukaci Jakadan Israela Ya Fice Daga Kasar Afrika
  • Anyi Jana’izar Mahaifiyar Nasiru El Rufai A Abuja Afrika
  • Kungiyar Kiristoci Ta Karyata Kubutar Da Mambobin Su A Kaduna Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.