Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028
Najeriya ta samu damar shiga gasar Beach Volleyball ta wasannin Olympics a karon farko a tarihin ƙasar.
Najeriya ta doke Morocco da ci 2-0, da maki 21-17 da 21-10, a wasan ƙarshe na mata na gasar **2026 African Beach Volleyball Nations Championship**, da aka gudanar a Alexandria, ƙasar Masar, ranar Asabar 22 ga Agusta.
Nasarar ta ba Najeriya damar samun gurbin shiga gasar Beach Volleyball ta wasannin Olympics da za a gudanar a Los Angeles a shekarar 2028.
Bayan nasarar, Shugaban Hukumar Kwallon Volleyball ta Najeriya (NVBF), Injiniya Musa Nimrod, ya bayyana samun tikitin a matsayin gagarumar nasara ga Najeriya baki ɗaya, bayan shekaru da dama ana fuskantar rashin sa’a a ƙoƙarin samun wannan gurbi.
Nimrod ya ce:
“Ina taya ’yan Najeriya murna tare da gode wa Allah. Wannan shi ne karo na huɗu da muka kai wasan ƙarshe; sau uku a baya mun zo na biyu.
“Allah ya sa a karo na huɗu muka samu nasara. Wannan ba nasarar Hukumar Volleyball ta Najeriya kaɗai ba ce, nasarar ƙasa baki ɗaya ce.”
Nimrod ya kuma tuna da tsawon shekaru 16 da hukumar ta yi tana jiran samun wannan gagarumar nasara.
Ya ce: “Ina so in bayyana cewa bayan shekaru 16, yau Allah ya ba hukumar damar cimma wannan nasara.”
Sakatare-Janar na CAVB Zone 3 shi ma ya yabawa Hukumar Kula da Wasanni ta Ƙasa (NSC) da kuma Kwanturolan-Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya, CGC Adewale Adeniyi, bisa irin goyon bayan da suke ci gaba da bai wa hukumar domin bunƙasa wasan Volleyball a Najeriya.


