Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sanda, Sojoji Da DSS Sun Ceto ‘Yan NYSC Da Aka Sace A Kogi Afrika
  • RUWASSA Ta Hada Masu Ruwa Da Tsaki Domin Inganta Aiwatar Da Shirin NG-SURWASH Afrika
  • Rundunar ’Yan Sandan Bauchi Ta Kama Dattijo Kan Zargin Cin Zarafin Yarinya ’Yar Shekara 8 Afrika
  • Damara Ya Tallafa Wa Gasar Karatun Al-Qur’ani Da Naira Miliyan Biyar A Bambam Afrika
  • Gwamna Inuwa Yahaya Ya Jaddada Haƙuri Da Fahimtar Juna A Siyasa Afrika

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Al’umma Su Kiyaye Doka Yayin Bikin Takutaha
Published: September 1, 2026 at 7:52 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ’yan sandan jihar Kano a Najeriya ta ce ta ɗauki tsauraran matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya yayin bikin Takutaha na shekarar 2026, wanda ake sa ran gudanarwa a yau Talata, 1 ga Satumba.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar Kano bisa yadda suka kasance suna gudanar da bikin cikin lumana, haɗin kai da bin doka a shekarun baya.

Bakori ya kuma gode wa sarakunan gargajiya, malaman addini, shugabannin al’umma da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki, bisa haɗin gwiwar da suke bai wa rundunar wajen tabbatar da zaman lafiya.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, rundunar ta ce ta tanadi matakan tsaro na musamman da suka haɗa da ayyukan leƙen asiri, sintiri na sa’o’i 24, binciken ababen hawa da mutane, da tura jami’an tsaro na musamman zuwa wuraren da za a gudanar da bikin.

Rundunar ta ce za a kuma sanya jami’an tsaro a hanyoyin shiga da fita da kuma wuraren da ake ganin za su iya zama barazana ga tsaro.

Kwamishinan ’yan sandan ya gargadi ’yan daba da masu tada zaune tsaye da su nisanci wuraren bikin, yana mai cewa rundunar ba za ta lamunci tashin hankali ko duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a ba.

Ya ce duk wanda aka kama yana karya doka za a gurfanar da shi gaban kotu domin fuskantar hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Rundunar ta kuma bukaci al’umma da su gudanar da bikin cikin lumana, su kasance masu bin doka, tare da gaggauta kai rahoton duk wani mutum ko abu da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa ko kuma ta layukan gaggawa na rundunar.

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta yi kira ga al’ummar jihar da su ba da cikakken haɗin kai domin ganin an gudanar da bikin Takutaha cikin zaman lafiya, farin ciki da annashuwa.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Shirye-Shirye

Post navigation

Previous Post: RUWASSA Ta Hada Masu Ruwa Da Tsaki Domin Inganta Aiwatar Da Shirin NG-SURWASH
Next Post: ’Yan Sanda, Sojoji Da DSS Sun Ceto ‘Yan NYSC Da Aka Sace A Kogi

Karin Labarai Masu Alaka

Sojoji Sunkai Farmaki Gidan Dan Adawa A Kasar Uganda Bobi Wine Afrika
Majalisar Tarayya Ta Amince Da Gyara Dokar Kasafin Kudi Labarai
Kasar Saudiya Ta Sanar Da Ganin Watan Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Isra’ila Zata Rusa Gidajen Da Suke Iyakarta Da Lebanon Labarai
Kungiyar ECOWAS Ta Koka Game Da Yawan Juyin Mulki A Kasashen Afirka Afrika
Ministan Harkokin Wajen Rasha Dana Iran Sun Tattauna Don Kawo Karshen Yaki A Gabas Ta Tsakiya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sanda, Sojoji Da DSS Sun Ceto ‘Yan NYSC Da Aka Sace A Kogi
  • Rundunar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Al’umma Su Kiyaye Doka Yayin Bikin Takutaha
  • RUWASSA Ta Hada Masu Ruwa Da Tsaki Domin Inganta Aiwatar Da Shirin NG-SURWASH
  • Rundunar ’Yan Sandan Bauchi Ta Kama Dattijo Kan Zargin Cin Zarafin Yarinya ’Yar Shekara 8
  • Damara Ya Tallafa Wa Gasar Karatun Al-Qur’ani Da Naira Miliyan Biyar A Bambam

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Najeriya: Ta Aiwatar Da Tsarin Ba Aiki Ba Albashi Ga Ma’aikata Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika
  • Kungiyar EU Zata Taimakawa Somalia Da Kudade Labarai
  • Sojojin Faransa Sun Karyata Zargin Bobi Wine Labarai
  • Afirka Ta Kudu Tace Bazata Yanke Alaka Da Iran Ba Afrika
  • Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Roger Lumbala Shekaru 30 Labarai
  • Liverpool Tayi Rashin Nasara A Wasanni Tara Wasanni
  • Najeriya Ta Bawa Dan Takarar Guinea-Bissau Mafaka Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.