Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Diphtheria: Mutane 23 Sun Mutu A Jihar Filato
Published: September 5, 2026 at 6:17 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Daga Zainab Babaji a Jos

A kalla mutane 23 sun rasa ransu, wassu 143 da ake zargin sun kamu da cutar ta diphtheria a fadin jihar Filato, cikin makonni biyu da suka gabata.

Kwamishinan lafiya na jihar Filato, Nicholas Baamlong ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Jos.

A cewar Ba’amlong, gwamnatin jihar da ma’aikatar lafiya sun kara kaimi wajen dakile yaduwar cutar.

Yace matakan da suka dauka sun hada da killace majinyata a asibitin Jamia’r Jos, JUTH, da asibitin kwararru ta jihar Filato, ana musu jinya.

Ba’amlong ya ci gaba da cewa cutar diphtheria cuta ce mai saurin yaduwa daga mutum zuwa mutum ta hanyar shakar numfashi, da duk wani ruwa daga jikin mai cutar, ha hanyar kusanci da shi.

Kwamishinan ya ce jihar Filato na fuskantar matsaloli wajen tabbatar da wadanda ake zargin sun kamu da cutar ne saboda rashin wadatattun wassu muhimman kayan aiki na musamman da ake bukata domin karbar samfuri zuwa dakunan gwaje-gwaje.

“Ya zuwa yanzu, muna da mutane 143 da ake zargin sun kamu da cutar, an kuma kashe mutane 23 a halin yanzu, tara a asibitin koyarwa na Jami’ar Jos, JUTH, da kuma asibitin kwararru na Filato, Jos,” in ji Baamlong.

Ya kara da cewa, babban kalubalen da ma’aikatar ke fuskanta biyo bayan bullar cutar sun hada da yadda wadanda suka kamu da cutar ke zuwa a makare da kuma samun maganin kashe kwayoyin cuta, domin cutar diphtheria na iya yaduwa cikin sauri ta hanyar saduwa, tari, atishawa da kusanci.

“Muna fuskantar kalubale game da cutar saboda ya kamata a tattara samfurin a cikin akwati na musamman domin mu aika don tabbatarwa, amma ba mu da irin wannan kwantena,” in ji shi.

Kwamishinan ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar ta kara kaimi wajen wayar da kan jama’a a matakin al’umma, tare da baiwa sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki su wayar da kan jama’a game da cutar da kuma hanyoyin hana yaduwarta.

“Ya zuwa yanzu mun kaddamar da yakin wayar da kan al’umma ta hanyar sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki don dakile yaduwar,” in ji Baamlong.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Shirye-Shirye

Post navigation

Previous Post: Athletic Club Ta Doke Atlético Madrid 3-0, Julian Alvarez Ya Koma Wasa
Next Post: Rikicin Aure: Albani Agege Ya Zargi Sheikh Gumi Da Boye Matarsa ‘Yar Morocco

Karin Labarai Masu Alaka

Hari Akan Wata Mashaya Ya Rutsa Da Mutane 9 A Afirka Ta Kudu Afrika
Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa Afrika
Shugaba Tinubu Yakarawa Mambobin ASUU Kashi 40 Na Albashi Najeriya
AIG Kwaimo Ya Kai Ziyarar Aiki Gombe, Ya Buƙaci Ƙara Ƙaimi A Yaƙi Da Ta’addanci Labarai
Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Afrika
Tinubu: Abba Magajin Aminu Kano Ne A Fagen Siyasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • PDP Zata Karbi Mulki 2027 Inji Shugabannin Jam’iyar Siyasa
  • TIC Dutse Ta Nemi Ƙarin Tallafin Gwamnatin Jigawa Don Faɗaɗa Ayyukanta Afrika
  • Harin Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Kakakin ‘Yan Tawayen M23 Afrika
  • FIFA, Ta Tabbatar Da Ranar Mika Sunayen ‘Yan Wasa AFCON 2025. Wasanni
  • An Kashe Mayakan Sakai 67 A Pakistan Sauran Duniya
  • Trump Zai Sasanta Tsakanin Masar Da Habasha Amurka
  • APC Ta Sauya Jerin ‘Yan Takararta Bayan Nazarin Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Fidda Gwani Afrika
  • Najeriya Da Poland Za Su Hada Kai Kan Tsaro da Bunƙasa Tattalin Arziki Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.