Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

Kotun Tarayya Ta Soke Tikitin Pantami, Ta Umarci PDP Ta Sake Zaben Fidda Gwani
Published: September 24, 2026 at 12:23 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: September 24, 2026

Kotun Tarayya da ke zamanta a Gombe ta umarci Jam’iyyar PDP da ta gudanar da sabon zaben fidda gwani domin fitar da ɗan takararta na kujerar gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2027.

Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta jagoranci shari’ar, bayan da Usman Aliyu Garry, Khamisu Ahmed Mailantarki da Abdulkadir Hamma Saleh suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar fitowar Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar na PDP.

Garry, Mailantarki da Abdulkadir sun ƙalubalanci fitowar Pantami bayan da jam’iyyar ta sanar da shi a matsayin ɗan takararta tilo a ranar 26 ga Yuni, 2026, yana mai cewa ba a gudanar da zaɓen fidda gwani yadda doka ta tanada ba.

Pantami, wanda a baya ya kasance ɗan takarar neman kujerar gwamna a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, ya koma PDP ne bayan da APC ta amince da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takarar da aka cimma matsaya a kansa.

Daga bisani, Pantami ya samu tikitin PDP ta hanyar amincewa da murya (voice affirmation) yayin zaɓen fidda gwamnan jam’iyyar da aka gudanar a watan Mayu.

Sai dai a hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, kotun ta umarci PDP da ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani, bisa bin ƙa’idojin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokokin zaɓe da suka dace.

Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Darakta Janar Charles Ebuebu Ya Jagoranci Taron Dabarun Karfafa Aikin Hukumar NBC
Next Post: Najeriya Da Amurka Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Bunƙasa Harkar Ma’adinai

Karin Labarai Masu Alaka

An Kama Masu Fasa Kaurin Gawayi A Malawi Afrika
Majalisar Dokokin Kamaru Ta Amince Da Wasu Sauye Sauye Afrika
Iran Da Amurka Zasu Kulla Yarjejeniyar Nukiliya Amurka
Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Christ Musa Ministan Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika
Shugaba Bola Tinubu Ya Saka Hannu A Dokar Zabe Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tinubu Na Kokarin Rage Tsadar Sufuri Ta Hanyar Shirin CNG Afrika
  • NAHCON Ta Kaddamar da Tawagar Malamai Afrika
  • Talauci Ya Hana Iyalan Ɗaliban Borno Da Aka Sace Zuwa Abuja Domin Zanga-Zanga Afrika
  • Congo Ta Kawo Karshen Cutar Kyandar Birai Afrika
  • Shugaban Ukraine Ya Tattauna Da Trump Akan Zaman Lafiya Amurka
  • “Hotuna” An Sako Daliban Makarantar St. Mary’s Su 100 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Kasar Ghana Ta Rage Farashin Cocoa Afrika
  • An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Mata A Najeriya NWFL 2025 Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.